Kwamishina ya rufe ma'aikata a waje saboda sun makara zuwa ofis a Legas

Kwamishina ya rufe ma'aikata a waje saboda sun makara zuwa ofis a Legas

- An hana wasu ma'aikatan hukumar Tsare-tare da cigaban birane na jihar Legas shiga aiki saboda sun makara

- Kwamishinan ma'aikatar , Dr Idris Salako ne ya bada umurnin inda ya koka kan yadda wasu daga cikin ma'aikatan ke sakaci da aiki

- Ya ce sun yi taro makonni uku da suka shude na cewa za a yi gyra amma duk da haka wasu ma'aikatan suna cigaba da wasa da aiki

- Salako ya ce akwai ma'aikat da dama da ba su zuwa aiki sai ranakun da suka yi nishadi sannan su tafi gida kafin lokacin tashi

Kwamishinan Tsare-tare da cigaban birane na jihar Legas, Dr Idris Salako, a ranar Juma'a ya bada umurnin a hana wasu ma'aikata shigowa ma'aikatar saboda sun makara zuwa aiki, News Wire ta ruwaito.

Daga bisani Salako ya bada umurnin a bawa dukkan ma'aikatan da suka makara takardar neman jin ba'asi wato kweri kan don sanin dalilin makararsu.

Kwamishina ya rufe ma'aikata a waje saboda sun makara zuwa ofis a Legas
Kwamishina ya rufe ma'aikata a waje saboda sun makara zuwa ofis a Legas. Hoto: @NewsWireNGR
Source: Twitter

Ya shaidawa kamfanin dillanci labarai, NAN, cewa mafi yawan ma'aikatan hukumar ba suna wasa da aikinsu.

KU KARANTA: Rashin tsaro: An maka Buhari da Makinde a kotu kan rikicin makiyaya a Oyo

"Su kan zo aiki ne a lokacin da suka nishadantu a duk ranar da suka ga dama kuma su kan tafi gida kafin lokacin tashi aiki wanda hakan ya saba dokar aiki.

"Na rufe wadanda su ke kan aiki da wadanda na tafi ba su wuraren aikinsu a lokacin.

"Za a bawa ma'aikatan takardar kweri saboda sakaci da aikinsu.

"Idan za ka iya tunawa makonni uku da suka gabata yayin wani taro an amince cewa za a sauya yanayin aiki domin tafiya da tsarin gwamna Babajide Sanwo Olu na kawo cigaba a Legas.

"Zuwa aiki a makare ya saba da abinda muka amince da shi yayin taron," ya shaidawa NAN.

DUBA WANNAN: Buhari bai taɓuka wani abin azo a gani ba a fannin tsaro, in ji Gwamna Ortom

Wakilin NAN da ya ziyarci ma'aikatar misalin karfe 10.55 na safe ya ruwaito cewa masu tsaron ma'aikatan sun rufe kofofi sun hada wadanda suka makara zuwa aiki shiga.

A wani labarin daban, Rundunar Sojojin Nigeria ta nada Mohammed Yerima a matsayin sabon direktan sashin hulda da jama'a, The Cable ta ruwaito.

Yerima, mai mukamin Brigedier-Janar zai maye gurbin Sagir Musa wanda ya kasance kakakin sojin na rikon kwarya tun shekarar 2019.

Kafin nadinsa, Yerima ya rike mukamin direktan sadarwa na tsaro da kuma mataimakin direkta a hedkwatar tsaro.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Source: Legit.ng

Online view pixel