Gwamnan Ebonyi ya fadi yadda ‘Buhari’ ya hada shi fada da PDP, ya shiga APC

Gwamnan Ebonyi ya fadi yadda ‘Buhari’ ya hada shi fada da PDP, ya shiga APC

- Gwamna Umahi ya ce Buhari ne dalilin da ya sa ya fice daga Jam’iyyar PDP a 2020

- Dave Umahi ya ce ya koma APC ne saboda ya na ganin darajar Shugaban kasar

- A cewarsa ya raba gari ne domin ‘Yan PDP su na so a rika sukar Shugaba Buhari

Premium Times ta rahoto Mai girma gwamnan Ebonyi, David Umahi, ya sake yin karin bayani game da abin da ya sa ya bar jam’iyyar PDP ya koma APC.

Gwamna David Umahi ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya kai wa takwaransa na jihar Jigawa, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar wata ziyara.

Umahi ya yi jawabi ne a gaban wasu magoya bayan jam’iyyar APC wajen kaddamar da wani titi da aka gina a garin Babura, ya ce Buhari ya sa ya bar PDP.

“Babbar matsalar PDP ita ce ana son kowa ya rika sukar shugaban kasa Muhammadu Buhari.”

KU KARANTA: Za mu gani, APC za ta kunyata Umahi a 2023 - PDP

“A matsayina na gwamna, shugabannnina su ne uwargidata da Mai girma Muhammadu Buhari, wanda shi ne shugaban kowa da kowa.” Inji David Umahi.

Ya ce: “Idan har an yi maka tarbiya, ka san cewa ba ka bukatar ka zagi babba da shugabanka.”

“Shugaban kasa ya cancanci girmama wa da goyon baya domin Najeriya da mutanen kasar ya sa a gaba. Lokacin da na ke PDP, (Buhari) ya taimaka mani.”

"Buhari mutum ne mai ganin girman kowane gwamna, mutumin da ya ba ya aika kowa ya yi fada da abokan gabansa. Ya cancanci goyon-baya da girmama wa”

KU KARANTA: APC ta na harin Gwamnonin PDP; Ifeanyi Ugwuanyi, Ben Ayade da Bala

Gwamnan Ebonyi ya fadi yadda ‘Buhari’ ya hada shi fada da PDP, ya shiga APC
David Umahi da Buhari Hoto: @DaveUmahi
Asali: Twitter

Mista Umahi wanda ya shiga APC domin ceto Ibo a babban zaben 2023, ya ce ba don Buhari ba, da gwamoni sun sha wahala, domin ya na tallafa wa kowa.

Gwamnan Jigawa ya gaskata abin da Umahi ya fada, ya fadi irin tallafin da gwamnatin tarayya ta ba jihohi.

David Umahi wanda ya lashe zaben gwamna har sau biyu a karkashin jam’iyyar PDP ya sauya-sheka zuwa jirgin APC a karshen shekarar da ta wuce.

Bayan wani lokaci da sauya-sheka, PDP ta yi magana game da labarin, ta ce ce Gwamna Dave Umahi bai rubuto takarda mai nuna ya koma APC ba.

Shugaban rikon kwarya na jam’iyyar PDP a jihar Ebonyi, Fred Udogu, ya ce za su koya wa gwamna David Umahi darasi a siyasa tun da ya tafi APC.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel