Jam'iyyar APC zata kunyata Umahi a 2023, in ji PDP

Jam'iyyar APC zata kunyata Umahi a 2023, in ji PDP

- Gwamna Umahi na jihar Ebonyi na son kujerar takarar shugabancin kasa a zaben 2023 in ji PDP

- APC zata bashi kunya shi bai sani ba, a cewar wani jigon a jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP

- Umahi ya bayyana cewa ya fice daga jam'iyyar PDP sakamakon rashin adalci da ake yi wa yan yankin kudu maso gabas

Jam'iyyar PDP ta ce jam'iyya mai mulki ta APC zata bawa gwamna Dave Umahi na Ebonyi a babban zabe mai gabatowa na 2023.

Umahi ya bayyana ficewa daga jam'iyyar PDP zuwa APC a ranar Talata, a zangon mulkin sa na biyu bayan an zabe shi karkashin inuwar jam'iyyar PDP.

Jam'iiyar APC zata kunyata Umahi a 2023, in ji PDP
Jam'iiyar APC zata kunyata Umahi a 2023, in ji PDP. Hoto: @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An yanke wa mutumin da ya datse kan dansa hukuncin kisa a Adamawa

Akwai yiwuwar Umahi na son takarar shugabancin kasa a zaben 2023, kuma yana neman jam'iyyar da zata bawa dan yankinsa takara ko zai samu gurbin tsayawa.

Sai dai ya karyata wannan batu a lokacin da ya yake bayani bayan komawarsa jam'iyyar APC, yake cewa, "na dawo wannan jam'iyya ne sakamakon irin rashin adalcin da ake wa yan yankin kudu maso gabas a PDP tun daga 1999 har yanzu."

KU KARANTA: Katin gayyatar ɗaurin auren Bashir El-Rufai da Nwakaego ya fito

Da yake jawabi a taron shugabannin PDP karo na 90 da ya gudana a hedikwatar jam'iyyar PDP a Abuja, shugaban kwamitin amintattu, Sanata Walid Jibrin ya ce, "ina tausaya masa."

"APC zata bashi kunya shi bai sani ba," a cewar sa.

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, gwamnatin Jihar Kogi za ta bullo da sabon haraji a kan kowanne gasashen burodi a jihar kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Ma'aikatar kasuwanci da masana'antun tace harajin zai taimaka wajen kara samun kudaden shigar da ake samu na cikin gida.

Amma, kungiyar masu gasa burodi reshen jihar sun bayyana cewa basu goyon harajin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel