Jam’iyyar PDP ta ce za ta koyawa Gwamnan jihar Ebonyi hankali a siyasa

Jam’iyyar PDP ta ce za ta koyawa Gwamnan jihar Ebonyi hankali a siyasa

- Bayan kusan watanni 2 da sauya-sheka, PDP ta ce Gwamna bai bar Jam’iyya ba

- Jam’iyyar PDP ta ce Dave Umahi bai rubuto takarda mai nuna ya koma APC ba

- Shugaban PDP ya ce Umahi ya dade da barin PDP, kuma za su kankare sunansa

Shugaban rikon kwarya na jam’iyyar PDP a jihar Ebonyi, Fred Udogu, ya ce kwanan nan za su cire sunan gwamna David Umahi daga cikin jerin ‘ya ‘yansu.

Daily Trust ta yi hira da Mista Fred Udogu inda ta rahoto shi ya na cewa David Umahi ya sauya-sheka ne da fatar baki kawai ba tare da ya rubuto masu ba.

Shugaban rikon kwaryan na PDP ya bayyana cewa a shirye jam’iyyar ta ke ta sake karbar David Umahi a duk lokacin da ya ga damar dawowa inda ya bari.

Fred Udogu ya ce PDP ba ta taba samun kanta cikin mummunan hali a jihar Ebonyi kamar yadda ta shiga a lokacin da ta ke hannun gwamna David Umahi ba.

KU KARANTA: Umahi zai iya takara a APC a 2023 - Buhari

Udogu ya yi wa jaridar bayanin shirin da ake yi na goge sunan Umahi daga rajistar jam’iyya.

Ya ce: “Babu wanda ya isa ya zauna a jam’iyyu biyu a lokaci guda. Kwanan nan za mu dauko takardar dake dauke da sunan ‘ya ‘yanmu, za mu cire sunan sa.”

“Bai fice daga PDP ba, ya bar jam’iyya ne kurum ta fatar baki, ya ce ya koma APC, amma za mu koya masa yadda ake canza jam’iyya da kyau.” Inji shugaban PDP.

“Babu maganar jam’iyyar PDP a lokacin da Dave Umahi ya ke nan.”

KU KARANTA: Idan PDP na so ta kunyata ni, ta ba Ibo takara a 2023 - Umahi

Jam’iyyar PDP ta ce za ta koyawa Gwamnan jihar Ebonyi hankali a siyasa
Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi Hoto: Nigerian Voice Daga; www.thenigerianvoice.com
Source: UGC

“Dave Umahi ya bar PDP tun 2017, kuma manya da shugabannin PDP na kasa sun san wannan.”

A farkon makon nan mu ka kawo maku wani rahoto cewa ana rade-radin wasu gwamnonin PDP suna harin sauya-sheka, za su tattara su koma APC kwanan nan.

Jigon APC a jihar Enugu, Ayogu Eze ne ya fito ya na cewa wasu gwamnonin Kudu maso gabas za su koma Jam’iyyar APC, amma Eze bai iya kama sunan gwamnonin ba.

Eze ya ce nan ba da dadewa APC za ta kara kafa wasu gwamnoni a Kudu bayan Dave Umahi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Newspaper

Online view pixel