Haramta Bitcoin: Kasar Amurka ce ta ankarar da CBN barnar da ake yi wa Nigeria

Haramta Bitcoin: Kasar Amurka ce ta ankarar da CBN barnar da ake yi wa Nigeria

- Muhimman bayanai na cigaba da fitowa dangane da dalilan hana cinikayya da sulallan "Crypto" a Nigeria

- Hukumar FBI ta kasar Amurka ta ankarar da gwamnatin tarayya cewa ana janye kudade daga kasashen turai tare da shigo da su Nigeria ta hanyoyin damfara

- Wata majiya ta bayyana cewa 'yan damfara na shigo da tsakanin $200m zuwa $300m zuwa Nigeria kowanne sati

Bayanai na kara fitowa akan dalilan gwamnatin tarayya na haramta amfani da sulallan yanar gizo yanar gizo da ake kira ''Crypto Currency", ko "Crypto a takaice, wajen duk wata hada-hadar cinikayya.

Babban kasa (CBN) ya fitar da sanarwar hakan a makon da ya gabata inda ya umarci dukkan bankunan da ke fadin kasar nan da su rufe wani asusu da ake amfani da shi wajen harka da ''Crypto''.

Wani rahoto da jaridar Thisday ta wallafa ya bayyana cewa hukumar tsaron kasar Amurka (FBI) ce ta yi wa gwamnatin tarayya korafi akan yadda 'yan Nigeria ke damfarar kasashen turai makudan miliyoyi.

FBI ta sanar da gwamnatin tarayya cewa miliyoyin daloli daga kasashen nahiyar turai na shigowa Nigeria ta barauniya kuma haramtacciyar hanya, wanda hakan kan iya haifar da babbar matsala ga tattalin arfzikin kasa.

Rahoton ya kara bayyana cewa FBI ta nuna cewa 'yan damfara da ake kira ''Yahoo Boys" sun damfari dumbin mazauna kasashen turawan yamma.

A cewar FBI, Yahoo Boys sun yi amfani da salo da dabarun damfara wajen tattare miliyoyin daloli da aka rabawa jama'a a matsayin tallafin annobar korona a kasashen turai tare da shigo da su Nigeria.

Haramta Bitcoin: Kasar Amurka ce ta ankarar da CBN barnar da ake yi wa Nigeria
Haramta Bitcoin: Kasar Amurka ce ta ankarar da CBN barnar da ake yi wa Nigeria
Source: UGC

Wata majiya a fadar shugaban kasa ta bayyana cewa, "masu damfarar turawan yamma suna shigo da kudin da yawansu ya kai tsakanin dala miliyan $200 da dala miliyan $300 a kowanne sati, ta hanyar amfani da crypto currency".

"An ankarar da gwamnatin tarayya da CBN akan abubuwan da ke faruwa wanda hakan shine yasa aka dauki matakin gaggawa domin ganin tattalin arzikin kasa bai samu wani lahani ba," kamar yadda Arise News ta rawaito.

Wata babbar matsala ta Crypto, a cewar gwamnatin tarayya, shine yadda yanzu masu garkuwa da mutane suka fara amfani da shi wajen karbar kudin fansa.

Jami'an tsaro suna matakura wahala kafin su iya gano mutumin da ya ajiye kudi ko kuma aka biya shi kudi ta hanyar amfani da Crypto saboda tsananin sirri da boye hanyoyin sauya sulallan zuwa takardu na zahiri bayan sun shiga bankuna.

Yayin wata tattaunawa da shugabar bankin nahiyar turai, Christine Lagarde, ta yi magana akan sulallan "bitcoin" inda ta ce, "wata kadara ce ta badini da ta zo da wasu matsaloli da suka hada da safarar kudi ta barayin hanyoyi, ina da ra'ayin cewa ya kamata a rufe duk baraka da kan iya bayar da damar aikata barna."

Legit.ng Hausa ta rawaito cewa gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya kai ziyara jihar Sokoto don jajantawa takwaransa, gwamna Aminu Waziri Tambuwal, bisa mummunar gobarar kasuwar da ta faru ranar Talata, 19 ga watan Junairu, 2021.

Yayin ziyarar, gwamna Wike ya bawa gwamnatin jihar Sokoto gudunmuwar milyan dari biyar (N500,000,000) domin sake gina kasuwar.

Hakazalika, Wike ya kai ziyara fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Abubuakar Sa'ad.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel