Jami’an Kwastam sun yi wa kamfanin Sin rangwamen shigo da kaya ta bayan-fage

Jami’an Kwastam sun yi wa kamfanin Sin rangwamen shigo da kaya ta bayan-fage

- Ofishin mai binciken kudi na Najeriya ya koka da raguwar kudin shiga

- Ana zargin Kwastam da yi wa kamfanonin kasar Sin rangwamen haraji

- Ya kamata ace an karbi kudin shigo da kaya a hannun kamfanonin Sin

A ranar Laraba, 3 ga watan Fubrairu, 2020, majalisar wakilan tarayya ta gano rangwamen fiye da Naira biliyan biyar da aka yi wa kamfanonin kasar Sin.

An yi wa jirgin kasar wajen wannan rangwame ne domin ya shigo da kayan gine-gine daga ketare duk da alkawarin biyan bashin da gwamnati tayi wa Sin.

Jaridar Tribune ta rahoto Wole Oke ya na sukar hukumomin da ke bada wadannan rangwame.

Honarabul Wole Oke ya yi wannan bayani ne a lokacin da ake sauraron korafin da ofishin mai binciken kudi na kasa ya aika wa hukumar kwastam.

KU KARANTA: An yi shekaru ba a dauki Ma’aikata ba – Hameed Ali zai yi bayani a Majalisa

‘Dan majalisar ya bayyana cewa wannan danyen aiki da ma’aikatu da hukumomi su ke yi, ya na jawo wa asusun gwamnatin tarayya asarar makudan kudi.

Shugaban kwamitin asusun gwamnatin na majalisar wakilai ya koka da yadda ake saba doka wajen bada rangwame da alawus ga kamfanonin kasashen waje.

Kamar yadda ‘dan majalisar ya bayyana, an yi wannan danyen aiki ne tsakanin 2014 zuwa 2020.

A dalilin wannan ne kwamitin majalisar ya bada umarni ga ministan kasuwanci da masana’antu ya fito da satifiket din da aka ba kamfanoni fiye da 600, 000.

KU KARANTA: Hukuma ta fara lakume kadarorin mutanen da aka samu ta 'haram'

Jami’an Kwastam sun yi wa kamfanin Sin rangwamen shigo da kaya ta bayan-fage
'Yan Majalisar Wakilai Hoto: Twitter @HouseNgr
Asali: Twitter

Oke ya ce ofishin mai binciken kudi na kasa watau OaAuGF ya koka da yadda ake samun karancin kudin shiga saboda wannan aiki da jami’an kwastam su ke yi.

A dalilin haka ne majalisa ta ke neman bayanai game da adadin jiragen ruwan kamfanonin da su ka tashi daga tashoshin Najeriya domin gano kudin da aka rasa.

Dazu kun ji cewa wani kwamitin majalisa wakilan tarayya ya na zargin an tafka satar man $20b, don haka aka sa rana za a binciki kamfanin NNPC da bankin CBN.

Majalisar ta ce tsakanin 2005 da 2019, gangunan danyen mai 320, 000, 000 su ka yi batar-dabo.

A jiya ‘Yan Majalisa su ka taso keyar manyan jami’an hukumar DPR a gaba, an yi masu tambayoyi, kuma shugaban DPR ya tabbatar da cewa ana satar danyen man kasar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel