Shugaban Najeriya ya yabi Matasa, ya yi kira su yi koyi da shi a tafiyar APC

Shugaban Najeriya ya yabi Matasa, ya yi kira su yi koyi da shi a tafiyar APC

- Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da matasan Jam’iyyar APC

- Buhari ya yi alkawarin ba matasan duk goyon bayan da su ke nema

- Shugaban kasar ya yi kira gare su da su tashi tsaye, a goga da su a APC

A ranar Alhamis, 4 ga watan Fubrairu, 2021, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ba matasan kasar nan tabbacin cewa zai mara masu baya.

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa zai ba matasa goyon bayan da su ke bukata domin yin nasara a siyasa da sauran harkokin da su ka sa gaba.

Kamar yadda hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmaad ya bayyana, Buhari ya bayyana wannan ne a lokacin da ya gana da matasan jam’iyyar APC a Aso Villa.

“Yayin da na ke sa ran cigaba da tattaunawa da kyau da matasa a kasar nan, ina so in tabbatar maku da cewa ni babban mai goyon bayanku ne.” inji Buhari.

KU KARANTA: Yadda aka yi wa Shugaban rikon kwaryan APC duka

Shugaba Buhari ya ce “Zan ba ku duka goyon baya domin ku yi nasara a harkar siyasa, aikin gwamnati, sha’anin wasanni, kasuwanci da duk wasu bangarori.”

“Domin na san cewa babu inda wannan kasar nan ta mu za ta je nan gaba idan babu matasa.”

“Na je Daura domin sabunta zama na ‘dan jam’iyyar APC. Ina kira a gare ku da ku yi haka. Imani da akidata su ne siyasa yawan mutane ce, karfi na ga jama’a.”

Buhari ya tuna wa matasa cewa a siyasa ana fara wa ne daga kasa, a kai mataki na sama. Sannan ya yaba da kokarin da su ke yi na kara wa jam’iyyar APC karfi.

Shugaban Najeriya ya yabi Matasa, ya yi kira su yi koyi da shi a tafiyar APC
Shugaban Najeriya Buhari da Matasa Hoto: www.channelstv.com/2021/02/04/i-will-offer-my-full-support-for-youths-to-grow-in-politics-buhari
Asali: UGC

KU KARANTA: Dabara Buhari yake yi a yunkurin ba su Buratai kujeru - PDP

“Kasar nan ta na bin matasa bashi, su yi amfani da dabararsu a kowane bangare – kiwon lafiya, kimiyya, ilmi, wasanni, harkar gona.” Inji shugaban Najeriyar.

A jiya kun ji cewa tsohon shugaban kungiyar Nigeria Economic Summit Group Sam Ohuabunwa ya bayyana aniyarsa na neman takarar shugaban kasa a 2023.

Fitaccen masanin ya yi hira da gidan talabijin na TV 360 Nigeria a makon da ya gabata, inda ya bayyana cewa zai so a ce ya zama magajin Muhammadu Buhari.

Sam Ohuabunwa mai shekara 70 ya na ganin cewa ya cancanci ya yi shugabancin Najeriya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng