Miloniyoyin Najeriya 5 masu karancin shekaru a 2021 da yadda suka tara dukiyarsu

Miloniyoyin Najeriya 5 masu karancin shekaru a 2021 da yadda suka tara dukiyarsu

- Akwai wasu matasan Najeriya da suka samu kudi nasu na kansu a kananan shekaru kuma za a iya kiransu miloniyoyi a 2021

- Marubuciya kuma mai tarin dukiya Linda Ikeji za a iya saka ta cikin wannan jerin a matsayin kallabi tsakanin rawuna

- Wadannan matasan masu kananan shekaru 'yan kasuwa ne kuma suna da labarai masu tarin mamaki dangane da dukiyarsu

Ana cewa komai tabarbarewar tattalin arzikin kasa, dole ne a samu wadanda suka samu riba a wannan lokacin.

Kamar yadda Legit.ng ta tattaro, ga miloniyoyi biyar matasa na Najeriya da tauraruwarsu ke haskawa tare da labaran yadda suka tara dukiyoyinsu.

5. Jason Njoku

Matashin mai shekaru 39 ya zo a lamba ta 5. Dan kasuwa ne kuma shine wanda ya samo Spark, wani kasuwanci mai jarin $2 miliyan kamar yadda nigeriafinder.com ta tabbatar.

Miloniyoyin Najeriya 5 masu karancin shekaru a 2021 da yadda suka tara dukiyarsu
Miloniyoyin Najeriya 5 masu karancin shekaru a 2021 da yadda suka tara dukiyarsu. Hoto daga entrepreneurs.ng, www.forbes.com ,guardian.ng
Asali: UGC

Mashiryin fina-finan ya kasance mai saka hannayen jari a manyan kasuwanci a Afrika. Tare da shi aka samar da iROKOtv.

KU KARANTA: Gwamnonin arewa sun yi magana da kakkausar murya a kan harin da ake kaiwa makiyaya

4. Linda Ikeji

Marubuciya Linda Ifeoma Ikeji ita kadai ce mace da ta shigo wannan jerin inda ta zama a lamba ta hudu.

Macen mai shekaru 40 ta mallaki gidan talabijin mai suna Linda Ikeji TV. Matar ta tamfatsa ginin gidanta mai kayatarwa a 2016 kuma an san ta da son kyale-kyale.

3. Igho Sanomi

Shine ya kafa Taleveras Group. Igho Sanomi da ne ga tsohon mataimakin sifeta janar na 'yan sanda kuma shine ya zo a mataki na uku.

Matashin dan kasuwan yana samun miliyoyin naira daga fannin lantarki, gine-gine da sauransu.

An gano cewa kamfaninsa yana ba babban kaso a wasu rijiyoyin man fetur guda biyu.

2. Ladi Delano

Kamar yadda mujallar Forbes ta bayyana, yana daga cikin wadanda ake hangowa a makomar kasuwancin kasar nan, Ladi Delano ya zo a lamba ta biyu a wannan jerin.

Ladi yana daga cikin manyan jiga-jigan da suka kafa Bakrie Delano Afrika mai darajar $1 biliyan.

Wannan kasuwancin ya mayar da hankali ne wurin hakar ma'adanai, aikin noma da kiwo da kuma bangaren man fetur da iskar gas.

1. Sijibomi Ogundele

Sijibomi Ogundele mai shekaru 36 matashi ne mai tarin dukiya. Dan kasuwa ne da ya mayar da hankali wurin harkar dillanci, siyarwa tare da gina gidaje.

KU KARANTA: Mutum 6 sun sheka lahira, 6 sun jigata bayan hatsarin da 'yan bindiga suka haddasa a titin Birnin Gwari

A wani labari na daban, rayuka biyu aka rasa yayin da wasu 'yan bindiga suka kai hari karamar hukumar Zaria da ke jihar Kaduna, Channels Tv ta wallafa.

'Yan bindigan sun kara da sace babura hudu daga karamar hukumar yayin da suke aika-aikar. Kamar yadda takardar da kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya fitar, 'yan bindigan sun kutsa kauyen inda suka kai hari gidan wani Abdulazeez Sani.

Sun sace matarsa mai suna Samira Abdulazeez tare 'ya'yansa biyu, Aliyu da Lawal Abdulazeez tare da wata mata Halima M. Sani da dan ta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel