Gumi: Masu fafutukar kafa kasar Biafra da Oduduwa basu da bambanci da Boko Haram

Gumi: Masu fafutukar kafa kasar Biafra da Oduduwa basu da bambanci da Boko Haram

- Shahararren malamin addinin Islama a Najeriya ya bayya cewa 'yan Najeriya basa son a raba kasar

- Malamin ya bayyana ra'ayinsa da cewa wasu tsiraru marasa amfani ne kadai ke son a raba kasar

- Ya kuma bayyana cewa duk masu son raba Najeriya basu da bambanci da 'yan Boko Haram

Wani shahararren malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi, ya ce masu neman kafa kasar Biafra da Oduduwa ba su da bambanci da ‘yan ta’addan kungiyar Boko Haram, Daily Trust ta ruwaito.

Gumi ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da BBC Pidgin a ranar Asabar yayin da yake sharhi kan halin rashin tsaro a kasar.

Malamin ya ce zai zama rashin adalci a ce ‘yan Nijeriya suna son a raba kasar saboda ayyukan wasu “ bata gari” wadanda kawai ke ingiza mugayen akidu da bukatunsu.

Malamin ya yi ikirarin cewa yawancin 'yan Najeriya suna son dunkulalliyar kasa inda zaman lafiya da daidaito ya yawaita.

KU KARANTA: Kasuwancin kiwon shanu ya fi na kudin intanet, in ji Adamu Garba

Gumi: Masu fafutukar kafa kasar Biafra da Oduduwa basu da bambanci da Boko Haram
Gumi: Masu fafutukar kafa kasar Biafra da Oduduwa basu da bambanci da Boko Haram Hoto: This Day News
Source: UGC

Ya ce: “Yawancin lokaci na kan ba da misali da Janar Murtala Mohammed, tsohon shugaban kasa daga Kano wanda tawagar Buka Suka Dimka ta kashe.

“Ya auri mata bayarbiya. Don haka, ina kuke son 'ya'yansa su tafi idan al'umma ta rarrabu?

“Shin za su kasance tare da Yarbawa ko kuma Hausawa a Arewa?

“Duba, mu manta da waɗannan samarin marasa amfani. Ba su da bambanci da wadannan makiyayan.

“Wadannan mutanen da ke neman kafa kasar Ododuwa, Biafra ko Arewa duk rukuni guda ne na mutanen da ke Boko Haram.

“Mafi yawan 'yan Najeriya suna son zama tare da sunan Najeriya. Kuma idan suna cikin shakka, bari mu gudanar da zaben raba gardama.

“Dubi zabe misali, miliyoyin kuri’u daga dukkan jihohin, walau daga APC ko PDP.

“Wannan yana nufin 'yan Nijeriya a shirye suke su kasance tare a dunkulewar Najeriya. Wannan zaben raba gardama ne wanda yake nuna cewa mutane a shirye suke.

KU KARANTA: Tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya dawo kan kafofin sada zumunta

“Don haka, duk wadannan matasa da ke ta hayaniya, ko Abubakar Shekau na Boko Haram, Nnamdi Kanu na IPOB da takwaransu na Ododuwa, su 'yan tsiraru ne daga cikin ‘yan Nijeriya da ke amfani da ra’ayin kabilanci, da na gargajiya da kuma neman lalata kasar.

“Amma zan iya tabbatar da cewa da gaske ne 'yan Najeriya suna son kasancewa tare cikin lumana. Sannan cikin aminci da daidaito. Babu wani yanki na Najeriya da ake yaudara.” In ji malamin.

A wani labarin, Shugaban 'yan ta'addan da ke zaune a Zamfara, Turji, ya yi barazanar gayyatar mayaka 'yan kasashen waje don tayar da zaune tsaye a Najeriya, HumAngel ta ruwaito.

Wani shugaban ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya, Kachalla Turji, ya ce kungiyarsa na iya yin kira ga goyon bayan kasashen waje don yaki da dagula Najeriya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel