Satar $20bn: ‘Yan Majalisa sun shake DPR, an aikawa NNPC, CBN sammaci
- Kwamitin binciken satar mai na majalisar wakilai ya na ta cigaba da aiki a Najeriya
- ‘Yan Majalisa sun taso keyar manyan jami’an hukumar DPR, ana yi masu tambayoyi
- Ana zargin an yi gaba da ganguna fiye da 300,000,000 na danyen mai na kusan $20bn
Labari ya zo mana daga jaridar Daily Trust cewa majalisar wakilan tarayya ta cigaba da binciken da ta ke yin a satar danyen mai na Dala biliyan 20.
Jaridar ta ce a ranar Laraba, 3 ga watan Fubrairun 2021 ne ‘yan majalisar tarayyar su ka zauna da jami’an hukumar DPR a aikin binciken da su ke yi.
‘Yan majalisar sun bada sanarwar cewa sun aikawa kamfanin man NNPC da babban bankin Najeriya watau CBN takarda cewa su bayyana gabansu.
Jami’an kamfanin mai na kasa na NNPC za su hallara a majalisar ne a yau ranar Alhamis, yayin da aka ware wa jami’an bankin CBN ranar Juma’a.
KU KARANTA: NNPC sun hako rijiyoyin danyen mai biyu a jihar Gombe - Minista
Mataimakin shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilai, Honarabul Peter Akpatason, da yake jawabi, ya ce sun duba duk takardun da ke gabansu.
Hon. Peter Akpatason ya ce a wajen wannan bincike da su ke yi, sun zo ga wasu abubuwa da ke bukatar masu ruwa da tsaki a harkar su yi karin bayani.
Kwamitin ya bukaci ganin duk wasu bayanai game da danyen man da aka dauko tsakanin 2005 da 2019.
Kamar yadda kwamitin ya bayyana, akwai bambanci tsakanin ainihin man da aka hako da abin da ake rubuta wa, wanda ke nuna ana satar danyen man.
KU KARANTA: Ana bibiyar dukiyoyin mutane da aka damkawa Gwamnati, za ayi gwanjonsu
Majalisa ta ce ba a san inda gangunan danyen mai 329,420,319 suka shige ba, wanda kudinsu ya kai $20b, ana maganar kimanin Naira tiriliyan 8 a 'yan shekaru.
Shugaban DPR, Sarki Auwalu ya tabbatar da hakan, ya ce ana satar danyen man ne a kasa, lokacin da aka tura man a bututu domin a kai su kasar waje a tace.
Akpatason ya ce kwamitinsu bai fito da niyyar yi wa wani mutum ko ma’aikata bita-da-kulli ba, ya ce su na kokarin shawo kan matsalar satar da ake yi ne.
A makon nan ne aka ji shugaban kamfanin NNPC, Mele Kolo Kyari ya na cewa Muhammadu Buhari ne Shugaban da aka fara yi da bai tsomawa NNPC baki.
Mele Kolo Kyari ya ce sun yi dace ganin yadda babu abin da ya shafi shugaba Buhari da aikinsu.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng