Majalisa ta aikawa Kwastam CG sammaci saboda karancin kananan ma’aikata

Majalisa ta aikawa Kwastam CG sammaci saboda karancin kananan ma’aikata

- Majalisa ta ce ta gano ana fama da karancin kananan Ma’aikata a Kwastam

- Kwamitin majalisar wakilai ya ce wani binike da ya yi ya nuna masa wannan

- Rabon da a dauki sababbin ma’aikata a hukumar kwastam tun shekarar 2012

Kwamitin da ke lura da aikin hukumar kwastam a majalisar wakilai ya aika wa shugaban hukumar na kasa, Hameed Ali, takarda ya bayyana gabanta.

Jaridar Daily Trust ta ce ana bukatar ganin Kanal Hameed Ali (mai ritaya) ne bayan hukumar kwastam ta shafe shekara da shekaru ba ta dauki ma'aikata ba.

Kwamitin majalisar ya ce an yi shekara 7 ba tare da gwamnati ta dauki sababbin kananan ma’aikata a hukumar ba, don haka ake neman karin bayani.

Wannan kwamiti ya bayyana cewa karancin kananan ma’aikata da kwastam ta ke fama da shi, ya na kawo mata matsaloli da barazana wajen gudanar da aiki.

KU KARANTA: Gangunan danyen mai miliyan 320 sun yi batar-dabo - Majalisa

Rahoton ya ce kwamitin ya gano hakan ne bayan ‘yan majalisar sun kai ziyara zuwa manyan ofisoshin shiyyoyi da na jihohi da sauran wuraren aikin kwastam.

Shugaban kwamitin kwastam, Honarabul Leke Abejide, ya bayyana cewa yawanci matsakaita da manyan ma’aikata ne su ka cika wuraren aikin da su ka gani.

A cewar Hon. Leke Abejide, rabon da a dauki sababbin ma’aikata a hukumar mai yaki da fasa-kauri a Najeriya tun 2012, shekaru fiye da bakwai da su ka wuce.

Da yake magana a ofishin kwastam na Abuja, Abejide ya ce ko da an dauki aiki sai dai ta bayan-fage.

KU KARANTA: Hameed Ali ya yi sababbin nade-naden mukamai a NCS

Majalisa ta aikawa Kwastam CG sammaci saboda karancin kananan ma’aikata
Kwastam CG, Hameed Ali Hoto: www.premiumtimesng.com
Source: UGC

“A ka’ida ya kamata duk shekara a rika daukar aiki. Ya za a sa mutum daya a wajen aikin mutane goma?” Ya ce ya ji za a dauki ma’aikata, amma ba na din-din-din ba.

Da aka nemi ayi irin haka da shugaban na kwastam a 2017, abin ya jawo sabani inda har ta kai Sanatoci sun kori Kanal Hameed Ali daga zauren majalisar tarayya.

An yi hakan ne bayan Hameed Ali ya hakikance a kan cewa ba zai sa kayan jami'an kwastam ba.

Hameed Ali wanda tsohon soja ne, yace bai san dokar da ta wajabta masa sanya khaki ba, amma ya ce ya cigaba da tuntubar lauyoyi domin ya ji abin da doka ta ce.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel