Makiyaya sun fayyace mani komai game da ta'addancin da yadda za a kawo karshen shi, in ji Sheikh Gumi

Makiyaya sun fayyace mani komai game da ta'addancin da yadda za a kawo karshen shi, in ji Sheikh Gumi

- Abun mamaki, wasu makiyaya da ake zargin yan bindiga ne a arewa na zargin gwamnati da rashin samar da kayayyakin more rayuwa

- Hakan ya bayyana ne sakamakon zagayen da shahararren malamin nan na Musulunci, Sheikh Abubakar Ahmad Gumi yayi

- Gumi ya ce wadannan makiyayan sun taba fadawa tarkon ta’addanci, garkuwa da mutane da sauran laifukan ta’addanci

A farkon shekarar nan, malamin addinin Islaman nan mazaunin Kaduna, Dakta Ahmad Gumi, ya fara aikin samar da zaman lafiya a garuruwan Fulani da aka sani da fashi da sace mutane.

Ya zuwa yanzu, Gumi ya ziyarci garuruwan da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, Gamagira a karamar hukumar Soba da Kidandan a karamar hukumar Giwa.

Ya zanta da jaridar Daily Trust kan abin da ya ba shi kwarin gwiwa har ya fara yada da'awar Musulunci da kuma samar da zaman lafiya.

Makiyaya sun fayyace mani komai game da ta'addancin da yadda za a kawo karshen shi, in ji Sheikh Gumi
Makiyaya sun fayyace mani komai game da ta'addancin da yadda za a kawo karshen shi, in ji Sheikh Gumi Hoto: Abubakar Ahmad Gumi
Asali: Twitter

Kan abunda ya bashi karfin gwiwa, malamin ya ce:

"Dalilin shine halin rashin tsaro a kasar. Wannan ya sanya muka yi nazarin tushen abubuwan da ke haifar da wadannan matsalolin, musamman daga wajen makiyaya. Mun fahimci cewa ba su da ilimin Islama da na zamani.

"Mun kuma fahimci cewa ba su da ilimin da ake bukata, musamman ilimin addini don haka muka yanke shawarar cewa ya fi kyau mu je mu tunkaresu a mazauninsu, maimakon jiran su zo su yi garkuwa da mutane, suna kashewa tare da yi wa mata fyade.”

KU KARANTA KUMA: Kotun koli ta yi watsi da bukatar iyalan Abacha na mallakar kudaden da ya sata

Game da yawan garuruwan da suka ziyarta, Gumi ya ce: So

"Ya zuwa yanzu, mun ziyarci garuruwa uku; daya a kusa da karamar hukumar Jere tare dahanyar babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja, wani a yankin Gamagira a karamar hukumar Soba sannan kuma na karshe shi ne Kidandan a karamar hukumar Giwa, wanda muka ziyarta a ranar Talata."

Kan ko yan bindigan sun mika masu makamai a yayin tattaunawarsu, Shehin malamin yace:

“Basu gabatar da kowani makami ba kuma ba ma bukatar su gabatar da wani a yanzu. Amma abin da muke yi yanzu yawon bude sanin juna ne, muna bude zukatansu da sauraron koke-kokensu yayin da muke ba su tabbacin cewa abubuwa za su inganta.

"Abin da ya ba mu mamaki shi ne sun yi alkawarin cewa wannan shi ne karshen tawayensu kuma sun shimfida wasu sharadai. Muna so mu nuna musu cewa aikin mu ba na soja bane amma namu shine tsarin addini da taimakon mutane don haka muke isar da garabasar zuwa garesu."

KU KARANTA KUMA: Jerin sunayen manyan attajiran Africa guda 10, Dangote, Adenuga da Rabiu na ciki

Shahararren malamin addinin musuluncin ya ci gaba da cewa yawancin makiyayan sun gudu zuwa cikin daji ne saboda zargin jinkirin gwamnati wajen magance tabarbarewar tsaro a yankin, kuma a kokarinsu na kare kansu, sai su kansu suka zama zama yan ta’adda.

Sheikh Gumi ya ce makiyayan ba su da bambanci da mutanen da ke zaune a cikin birni da birane saboda wasu daga cikinsu suna magana da harshen Turanci da kyau.

Ya kara da cewa:

"Da muka yi magana da su, sai su ka ce laifin gwamnati ne. To, dole ne a zargi gwamnati saboda suna bukatar daukar kwararan matakai don ganin cewa akwai abubuwan more rayuwa a yankinsu; ba su da wutar lantarki, ko ruwa babu, babu wani abu da ke nuna kasancewar gwamnati a wurin. Don haka wadannan su ne abubuwan da ya kamata gwamnati ta yi don kawo karshen wannan rashin tsaro.”

A baya mun ji cewa malaman addinin Kirista a arewacin kasar sun jinjinawa Sheikh Ahmad Gumi kan da'awar zaman lafiya da yake yawon yi a dazukan Kaduna.

Gumi dai na bi mazaunin yan ta'adda yana wayar masu da kai a kan bukatar rungumar zaman lafiya a kokarinsa na kawo karshe kashe-kashe da fashi a Kudancin Kaduna.

Fasto Yohanna Baru ya ce yunkurin Gumi na yin da'awar zai taimaka sosai wajen daidaita matsalar tsaro a kasar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel