Kotun koli ta yi watsi da bukatar iyalan Abacha na mallakar kudaden da ya sata

Kotun koli ta yi watsi da bukatar iyalan Abacha na mallakar kudaden da ya sata

- Kotun koli ta sake sauraron wani shari’a da ke da nasaba da kudaden Abacha da ke asusun bankin waje

- Kotun ta bayar da dalilan da yasa ba za ta iya goyon bayan masu karar ba

- Alkalin kotun kolin, Justis Ejembi Eko, ya bayyana aibin karar

Kotun koli ta yi watsi da wani kara da iyalan Sani Abacha suka shigar inda suka nemi a mallaka masu kudaden da ke asusun bankinsa na kasar waje.

An tattaro cewa tsohon Shugaban kasar a mulkin soja, Janar Sani Abacha ya

wawure tare da adana kudade a wasu bankunan kasashen waje kafin rasuwarsa a ranar 8 ga Yunin 1998.

Kotun koli ta yi watsi da bukatar iyalan Abacha na mallakar kudaden da ya sata
Kotun koli ta yi watsi da bukatar iyalan Abacha na mallakar kudaden da ya sata Hoto: Rachel Carrera, Issouf Sanogo
Source: UGC

KU KARANTA KUMA: Karon farko a shekarar 2021: Babu wanda ya kamu da cutar COVID-19 a Lagos

Kotun a hukuncin da ta yanke a ranar Juma’a, 22 ga watan Janairu, ta zartar da cewa karar da Ali Abacha, kanin marigayi shugaban kasar ya shigar ba ta da inganci, jaridar The Nation ta ruwaito.

Kwamitin mutum biyar na kotun, a hukuncin da suka yanke baki daya, sun bayyana cewa karar Ali Abacha ya saba doka kamar yadda aka fara a watan Afrilun 2004 a Babbar Kotun Tarayya da ke Kaduna.

Kotun ta yanke hukuncin cewa shari’ar ba ta bambanci da ta wani dan tsohon shugaban, Abba Mohammed Sani, wanda tun farko kotun koli ta yi watsi da shi a ranar 7 ga Fabrairu, 2020.

A cewar Jaridar Premium Times, Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun ce ta shirya hukuncin, amma mai shari’a Ejembi Eko ya karanta.

KU KARANTA KUMA: Jerin sunayen manyan attajiran Africa guda 10, Dangote, Adenuga da Rabiu na ciki

A wani labari na daban, hadimin shugaban kasar Najeriya, Bashir Ahmaad, ya jawo abin magana da ya tsokani tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.

Bashir Ahmaad wanda ya na cikin masu taimaka wa Muhammadu Buhari wajen yada labarai, ya yi wa Atiku martani bayan ya taya Joe Biden murna.

A jawabin da Alhaji Atiku Abubakar ya yi, ya roki sabon shugaban kasa Biden, ya cire takunkumin da aka sa wa ‘Yan Najeriya na zuwa Amurka.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel