Jerin sunayen manyan attajiran Africa guda 10, Dangote, Adenuga da Rabiu na ciki

Jerin sunayen manyan attajiran Africa guda 10, Dangote, Adenuga da Rabiu na ciki

Aliko Dangote na Najeriya shine mai kudin Afrika kuma har yanzu shine kan wannan matsayi tsawon shekaru 10 a jere, kamar yadda mujallar Forbes ta biloniyanfrika ta 2021 ta saki a ranar Juma’a.

Har ila yau, Mike Adenuga na kamfanin Globbacom, da Abbdulsamad na kamfanin BUA duk sun samu shiga jerin masu kudin Afrika inda suka fada rukunin biyar da shida.

Mujallar Forbes ta bayyana cewa, a Afirka, kamar sauran wurare a duniya, mawadata sun fito lafiyar Allah daga annobar.

Ta bayyana cewa biloniyan nahiyar guda 18 suna da kimanin $4.1bn, kaso 12 cikin dari fiye da shakara daya da ta gabata, , wanda kuma suna kan gaba ne ta hanyar kasuwar hadahadar hannayen jari ta Najeriya.

Jerin sunayen manyan attajiran Africa guda 10, Dangote, Adenuga da Rabiu na ciki
Jerin sunayen manyan attajiran Africa guda 10, Dangote, Adenuga da Rabiu na ciki Hoto: @GuardianNigeria
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Bayan kamuwa da corona: IMN na so a gaggauta sakin Sheikh Zakzaky da matarsa

“Tsawon shekaru 10 a jere, Aliko Dangote shine mutumin da ya fi kowa kudi a Nahiyar, wanda ya mallaki $ 12.1bn, wanda ya karu da $ 2bn daga jeren bara, saboda karuwar kusan kashi 30 cikin 100 na farashin simintin Dangote, kadararsa mafi daraja a yanzu,” cewar Forbes a cikin rahotonta.

Jerin sunayen ya bayyana mutum na biyu da ya fi kowa kudi a Afirka a matsayin Nassef Sawiris na Masar, wanda mafi yawan dukiyar sa ta kasance kusan kashi shida cikin dari na kamfanin kera kayayyakin wasanni Adidas.

Mutum na uku ita ce Nicky Oppenheimer ta Afirka ta Kudu, wacce ta gaji hannun jari a kamfanin DeBeers na lu'u-lu'u kuma ta ci gaba da gudanar da kamfanin har zuwa 2012.

Lokacin ne ta sayar da kashi 40 na hannun jarin danginta a DeBeers ga babban kamfanin hakar ma'adinan na AngloAmerican a kan $ 5.1bn.

Mujallar ya kuma kawo ccewa wanda ya fi kowa samun riba a wannan shekarar shi ne wani hamshakin attajiri dan Najeriya, Rabiu, Punch ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Dakarun rundunar sojin Najeriya sun ragargaji yan Boko Haram, sun kashe mutum 5

Rahoton ya ce, “Abin birgewa shi ne, hannun jarin kamfaninsa na simintin BUA, wanda aka sanya a kasuwar hadahadar hannayen jari ta Najeriya a watan Janairun shekarar 2020, ya ninka sau biyu a cikin shekarar da ta gabata.”

Hakan ya sa dukiyar Rabiu ta haura da kashi 77 na ban mamaki, zuwa dala biliyan 5.5, inda ya kara da cewa, Rabiu da dansa sun mallaki kusan kashi 97 na kamfanin.

A gefe guda, al'amuran siyasa a kasar Amurka sun dauki wani sabon salon tarihin yayin da Joe Biden ya zama shugaba mafi yawan shekaru a tarihin Amurka.

Dan jami'iyyar Democrat din, da aka rantsar ranar Laraba, 20 ga Janairu, a matsayin shugaban Amurka na 46. Abun ban sha'awa ya zama na 15 a jerin mataimakan shugaban kasa da suka dare shugabancin kasar Amurka.

Legit.ng ta tattaro jerin mataimakan shugabannin Amurka da suka dare shugabancin Kasar, ko dai bayan mutuwar na kan karagar ko ta har zabe ko kuma murabus.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel