An rantsar da Joe Biden matsayin shugaban kasan Amurka na 46

An rantsar da Joe Biden matsayin shugaban kasan Amurka na 46

- Tsohon mataimakin Barack Obama, Joe Biden, ya zama shugaban kasar

- Joe Biden ya kwashe shekaru 36 a matsayin Sanata kafin ya yi mataimakin shugaban kasa na shekara 8

- Ya kayar da Donald Trump a zaben da ya zama tarihi a demokradiyyar kasar

An rantsar Joe Biden a matsayin shugaban kasar Amurka na 46 a ranar Laraba, 20 ga watan Junairu, 2021, a harabar majalisar dokokin kasar, Capitol.

Hakazalika an rantsar da abokiyar tafiyarsa na zaben ranar 3 ga Nuwamba, 2020, Kamala Harris.

Shugaban Alkalan Amurka, CJ John Roberts ne ya rantsar da shugaban.

Joe Biden wanda ke da shekara 78 da haihuwa ya zama shugaban Amurka mafi shekaru a tarihi, yayinda mataimakiyarsa, Kamala Harris, ta zama macen farko da ta zama mataimakiyar shugaban kasa a tarihin kasar.

Daga cikin wadanda suka halarci taron ranstarwan akwai tsaffin shugabannin kasar Amurka, Barack Obama, Bill Clinton da George Bush.

Hakazalika mataimakin Trump, Mike Pence, ya halarci taron bayan baran-baran da maigidansa.

KU DUBA: Abubuwan da Trump ya fadawa Magoya bayansa da ya bar fadar White House

An rantsar da Joe Biden matsayin shugaban kasan Amurka na 46
An rantsar da Joe Biden matsayin shugaban kasan Amurka na 46
Source: Getty Images

KU KARANTA: Abubuwan da Trump ya fadawa Magoya bayansa da ya bar fadar White House

Mun kawo muku rahoton cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump, yayi fitarsa na karshe a matsayin shugaban kasar daga fadar White House.

Trump ya tashi cikin jirgin Marine 1 daga White House zuwa Joint Base Andrews inda aka shirya masa walimar kare wa'adin mulki sannan ya garzaya garinsa na Florida.

Donald Trump a ranarsa ta karshe a ofishin shugabancin Amurka ya yi wa sama da mutane 100 afuwa, ciki har da mawakn Amurka, Lil Wayne da Kodak Black.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel