Joe Biden ya zubar da hawaye lokacin da ya tuna da ‘dansa a tsakiyar jawabinsa

Joe Biden ya zubar da hawaye lokacin da ya tuna da ‘dansa a tsakiyar jawabinsa

- Joe Biden ya yi kuka a lokacin da ya ke yi wa Delaware jawabin sallama

- Biden ya ce tuna wa da ‘dansa ne ya sa ya zubar da hawaye gaban kowa

- Ana rade-radin ‘Ya ‘yan Trump ma sun barke da kuka da za su bar daula

Sabon shugaban kasar Amurka, Joe Biden, ya yi kuka a lokacin yake barin Delaware, ya na shirin zuwa birnin Washington inda za a rantsar da shi.

Rahotanni sun bayyana cewa Joe Biden ya yi kuka ne a ranar Talata, 19 ga watan Junairu, 2021, ya na tsakiyar jawabin ban-kwana a Wilmington.

Biden ya ce hawaye sun zubo masa ne a sakamakon tuna wa da ‘dansa wanda ya rasu, Marigayi Beau.

Joe Biden mai shekara 77 ya ce da-na-saninsa daya a Duniya shi ne da ya ga Beau bai cikin wurin taron da ya ke yi wa mutanensa na gida sallama.

KU KARANTA: Joe Biden ya karya tarihin da Donald Trump ya kafa a 2017

Joe Biden ya zubar da hawaye lokacin da ya tuna da ‘dansa a tsakiyar jawabinsa
'Ya 'yan Trump su na kuka Hoto: www.dailymail.co.uk
Asali: UGC

Ya na zubar da hawaye, Biden ya ce:

“Ina mai matukar alfaharin in tsaya nan a dakin shugaba Beau Biden. Jama’a maza da mata, abu daya da na ke da-na-sani shi ne da aka ce ba ya nan.”

Beau Biden shi ne babban 'dan sabon shugaban kasar, tsohan soja ne kuma 'dan siyasa ya rasu a 2015.

A jawabin na sa, Biden ya bayyana yadda yake kaunar Delaware a zuciyarsa, ya ce idan ya mutu za a rubuta sunan garin na sa a jikinsa, a birne shi da shi.

A gefe guda, Daily Mail ta rahoto cewa ‘ya ‘yan Donald Trump sun yi kuka a lokacin da suka taru, za suyi wa jama’a ban kwana a ranar Laraba da safe.

KU KARANTA: Abubuwan da Trump ya fadawa Magoya bayansa da ya bar White House

Joe Biden ya zubar da hawaye lokacin da ya tuna da ‘dansa a tsakiyar jawabinsa
Joe Biden ya na kuka Hoto: Twitter; @JoeBiden
Asali: Twitter

Jaridar ta ce an hangi Ivanka, Don Jr, Eric, da Tiffany suna yunkurin tare hawaye ya na kwarara a fuskarsu yayin da mahaifinsu Donald Trump yake jawabi.

Donald Trump ya godewa iyalinsa da sauran abokan arziki da su ka taimaka wa gwamnatinsa a shekaru hudu da ya yi ya na jagorantar sha’anin Amurkawa.

Dazu kun ji sabon shugaban kasa Joe Biden ya yi kumallo da wasu dokoki a ranar farkonsa a ofis.

Wadannan dokoki dai-daya har 17 da Joe Biden ya rattaba wa hannu jiya za su shafe manufofin gwamnatin Donald Trump wanda Biden ya ke adawa da su.

Za a ajiye maganar hana wasu kasashe zuwa Amurka, kuma kasar ta koma cikin kungiyar WHO.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng