'Yan bindiga sun kashe mai unguwa da wasu mutum 3 a Kaduna

'Yan bindiga sun kashe mai unguwa da wasu mutum 3 a Kaduna

- An kashe mai unguwa da wasu mutane 3 a wurare daban daban a Jihar Kaduna

- Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ya tabbatar da lamarin da yammacin Alhamis

- Gwamna El-Rufai ya aike da ta'aziyya ga iyalan mamatan tare da sa jami'an tsaro tsaurara bincike

'Yan bindiga sun kashe Mai Unguwa a kauyen Baranje da ke karamar hukumar Chikun a Jihar Kaduna, tare da wasu mutum uku, The Nation ta ruwaito.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, wanda ya bayyana lamarin da yammacin Alhamis, ya ce jami'an tsaro sun bada rahoton kashe mutane 4 a wasu yankunan kananan hukumomin Giwa, Chickun da Igabi.

'Yan bindiga sun kashe mai unguwa da wasu mutum 3 a Kaduna
'Yan bindiga sun kashe mai unguwa da wasu mutum 3 a Kaduna. Hoto: TheNationNews
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Yadda matashi ya yi garkuwa da mahaifinsa ya karbi naira miliyan 2 kuɗin fansa

A cewar Aruwan: "A kauyen Baranje kusa Bukuru a karamar hukumar Chikun, an kashe mutane biyu, Dogara Yahaya, Mai unguwar Baranje da wani Reuben Adamu.

"A Unguwan Sada a karamar hukumar Giwa, yan bindiga sun kashe wani Ibrahim Salisu bayan sun yi yunkurin garkuwa da shi.

"Haka zalika, an kashe wani makiyayi, Abdullahi Saleh a hanyar Kangimi, hanyar Kaduna - Jos a karamar hukumar Igabi.

KU KARANTA: Wanda na fara sace wa shine tsohon saurayi na da ya ƙi aure na, in ji mai garkuwa, Maryam

"Gwamna Nasir El-Rufai ya samu wannan rahoton da alhini, ya kuma mika ta'aziyyar sa ga iyalan wanda abin ya shafa, tare da yin addu'a Allah ya ji kansu. Ya kuma sa jami'an tsaro su tsananta bincike kan lamarin.

"Za a girke jami'an sojin sama da na kasa a Birnin Gwari, Giwa da Igabi, har zuwa Jihar Niger."

A wani labarin nan daban, Gwamnatin Jihar Kano ta umurci ma'aikatanta a jihar su zauna gida a matsayin wani mataki na dakile yaduwar annobar korona karo na biyu a jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnatin ta kuma bada umurnin rufe dukkan gidajen kallo da na yin taro a jihar sakamakon karuwar adadin masu dauke da kwayar cutar COVID 19 a jihar.

Kwamishinan watsa labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya sanar da sabbin dokokin yayin taron manema labarai da ya kira a ranar Talata inda ya ce an dauki matakin ne yayin taron masu ruwa da tsaki da aka yi a ranar Litinin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel