Sheikh Dahiru Bauchi ya gargadi gwamnoni game da tsangwamar almajirai

Sheikh Dahiru Bauchi ya gargadi gwamnoni game da tsangwamar almajirai

Fitaccen shehin Malamin darikar tijjaniyyah, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya shawarci gwamnonin yankin Arewacin Najeriya da su daina tsangwamar almajirai.

Daily Trust ta ruwaito Dahiru Bauchi ya yi kira ga gwamnonin su dakatar da duk wani tsari da suka bullo da shi da zai cutar da almajirai ko ya kuntata rayuwarsu.

KU KARANTA: Zaben gwamnan Ondo da Edo: Tsohon shugaban APC ya fallasa yan takarar da Buhari ke goyon baya

Malamin ya bayyana haka ne yayin rufe tafisirin Al-Qur’anin bana da ya gudanar a gidansa dake garin Bauchi, inda yace abin da gwamnonin suke yi ya saba ma dokar kasa.

Sheikh Dahiru Bauchi ya gargadi gwamnoni game da tsangwamar almajirai
Sheikh Dahiru Bauchi
Asali: Facebook

A cewarsa, ya za’a yi yan kasa suna da daman zuwa ko ina neman ilimi, amma a ce an hana ma almajirai wannan daman? Don haka yace yin haka ya saba ma kundin tsarin mulkin Najeriya.

Malamin ya cigaba da fadin kundin tsarin mulki ya baiwa kowa daman zama a duk garin da yake so ba tare da nuna bambanci ko wata matsala ba don ya gudanar da addininsa.

Saboda haka ya gargadi gwamnoni su daina korar almajirai daga garuruwansu, idan kuma ba haka ba za su fuskanci fushin Ubangiji.

Gwamnonin Arewa sun dauki gabarar kawo karshen almajiranci, don haka suke amfani da daman yaduwar Coronavirus wajen kwashe almajirai tare da mayar da su jahohinsu na asali.

Gwamnatin jahar Kaduna ce ta fara wannan aiki, inda ta kwashe fiye da almajirai 30,000, wanda ta mayar da su jahohin Kano, Katsina, Jigawa da sauran sassan Arewa.

Kazalika ita ma jahar Kano ta mayar da almajirai ga jahohinsu, wanda dalilin haka aka samu karuwar cutar Coronavirus a Kaduna, inda aka samu fiye da almajirai 15 suna dauke da cutar.

A wani labari kuma, yayin da ma’aikatan kiwon lafiya ke shirin shiga yajin aiki a Kaduna, gwamnati ta ce za ta bude cibiyoyin kiwon lafiyarta tare da kare ma’aikatan dake son zuwa aiki.

Gwamnatin ta bayyana haka ne a matsayin martani ga kokarin shiga yajin aiki da ma’aikatan ke yi, inda ta ce ba za ta lamunci duk wani bita da kulli daga wajen ma’aikatan ba.

Don haka tace bata amince da yajin aikin ba, kuma duk wanda bai je aiki ba ya yi asarar aikinsa kenan domin kuwa za’a dauki sunan kowanne ma’aikaci a ma’aikatar kiwon lafiya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel