Sheikh Dahiru Bauchi ya ce a daina musafaha saboda coronavirus

Sheikh Dahiru Bauchi ya ce a daina musafaha saboda coronavirus

Babban malamin addinin musulunci kuma shugaban mabiya Darikar Tijjaniyya a Najeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya bukaci jama’ar kasar da su bi umurnin likitoci su daina musafaha a tsakaninsu domin guje wa kamuwa da cutar Coronavirus.

Shehin malamin ya bayyana hakan ne bayan sanarwar da suka fitar na soke taron maulidin Sheikh Ibrahim Nyass da za a yi a Abuja da Sokoto sakamakon yaduwar cutar ta Coronavirus.

Dahiru Bauchi ya bayyana cewa an jingine taron maulidin ne domin yadda annobar ke yaduwa a makwabtan Najeriya sannan kuma cewa taron ba na yan Najeriya kadai bane.

Sheikh Dahiru Bauchi ya ce a daina musafaha saboda coronavirus
Sheikh Dahiru Bauchi ya ce a daina musafaha saboda coronavirus
Asali: Twitter

Ya ce mutane daga kasashen duniya kan shigo domin halartan taron maulidin amma yanzu babu hali don an rufe filayen jiragen sama tare da hana taron jama’a a wasu kasashen.

Ya jadadda cewa sai lokacin da annobar ta kau sannan za a gudanar da taron.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Legas ta hana sallar Juma’a na tsawon makonni 4 saboda Corona

Da farko dai mun ji cewa Khalifa Shehu Ahmad Tijjani Inyass ya bada sanarwar cewa an dage taron maulidi Shehu Ibrahim Inyass wanda kungiyar Majm'ul Ahbabu Shehu Ibrahim za ta shirya a garin Sokoto.

Sanarwar ta fito ne daga bakin mai magana da yawun Faila Maulana Sheikh Mahi Cisse a cikin wani dan gajeren sakon murya.

A cikin jawabin Sheikh Mahi Cisse, ya bayyana cewa Khalifa Shehu Tijjani Inyass ya bada izinin dage taron ne saboda barkewar cutar coronavirus wacce ta addabi al'ummar duniya baki daya.

Ya kara da kira ga kungiyar a kan ta gaggauta dakatar da dukkan shirye-shiryen maulidin nata.

A wani labarin kuma, mun ji cewa Kwamitin shugaban kasa dake yaki da yaduwar cutar Coronavirus ta kafa wata karamar kwamiti wanda za ta tattauna da shuwagabannin addinai daga bangarorin addinin Musulunci da kuma Kiristanci don duba yiwuwar kulle wuraren ibadu.

Ministan watsa labaru, Lai Muhammad ne ya bayyana haka yayin da yake bayar da jawabi game da shirye shiryen kwamitin a gidan talabijin na NTA, inda yace ba kai tsaye gwamnati za ta rufe wuraren ibada ba, har sai ta samu goyon bayan shuwagabannin addinai.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng