Kukah: Jigon APC ya zargi JNI da kokarin hada rikicin addini, ya roki Buhari da Tambuwal su shiga lamarin
- An yi kira ga Shugaba Buhari da gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal a kan su shiga tsakani a kan lamarin Bishop Kukah da majalisar JNI
- Jigon APC Cif Frank Kokori ne yayi rokon gaggawan a ranar Talata, 12 ga watan Janairu
- A cewar dattijon, sakataren kungiyar addinin Musuluncin na kokarin zuga rikicin addini a kasar
A yayinda ake tsaka da fafatawa da Bishop Matthew Hassan Kukah, Cif Frank Kokori ya yi kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamna Aminu Tambuwal da su shiga cikin lamarin.
Jigon na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Delta ya yi wannan rokon a wata hira da jaridar Triune a daren ranar Talata, 12 ga watan Janairu.
Dattijon ya bukaci Shugaban Najeriya da gwamnan da su dakatar da Khalid Abubakar Aliyu, sakatare-janar na kungiyar JNI daga zuga Musulmai a kan Kukah domin hana rikicin addini.
Kokori ya yi gargadi a kan rikicin addini da ka iya barkewa, inda ya kara da cewa hakan na iya zama babban hatsari ga Najeriya.
KU KARANTA KUMA: Rayuwa ba tabbas: Labarin matashin da ya yi hasashen mutuwarsa ya girgiza jama'a
Da yake ci gaba da martani Kokori ya bayyana mummunan fasara da gangan da kungiyar ta yiwa sakon kirsimetin babban faston a matsayin cin amana.
Jigon na APC ya yi bayanin cewa bayan ya gama karanta sakon, ya rasa gano wani waje inda malamin ya yi batanci ga Musulunci ko Musulmai. Ya bukaci Buhari da Tambuwal da su yi kira ga Dr Aliyu don kada ya haddasa rikicin addini a kasar.
A gefe guda, fadar shugaban kasa ta yi tsokaci kan bukatar da wata kungiyar Musulmai a Sokoto ta yiwa Bishop Matthew Kukah cewa ya janye maganar da yayi ko kuma ya tattara inasa-inasa daga jihar Sokoto.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, yace wannan ba daidai bane kuma hakan ya sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya.
KU KARANTA KUMA: Abubuwan da ya kamata ku sani game da ma'auratan da ake zargin sun yi auren zobe a Kano
Garba Shehu ya bayyana hakan a jawabin da ya saki da yammacin Laraba mai taken, "Wajibi ne a rabu da Fada Kukah yayi addininsa da siyasarsa."
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng