Yanzu-yanzu: An tsige Donald Trump matsayin shugaban kasa karo na biyu

Yanzu-yanzu: An tsige Donald Trump matsayin shugaban kasa karo na biyu

Majalisar dokokin kasar Amurka ta tsige shugaban kasa, Donald Trump, a matsayin shugaba karo na biyu cikin wa'adinsa na farko.

Trump yanzu ya zama shugaban Amurka na farko a tarihi da aka tsige sau biyu.

A kuri'un da yan majalisan suka kada na tsigeshi, wadanda suka amince da a tsige Donald Trump sun samu rinjaye.

Daga cikin wadanda suka amince a tsigesa akwai yan jam'iyyarsa ta Republican 10.

Ga yadda sakamakon ta kasance:

Wadanda suka amince a tsigeshi: 232

Wadanda suka zabi kada a tsigeshi: 197

Yanzu za'a garzaya da lamarin gaban majalisar dattawa wadanda zasu sake kada kuri'a kan rattafa hannu kan wannan tsigewa da aka yi masa.

Idan majalisar dattawa ta amince a tsigeshi, ba zai sake iya takaran kujeran shugaban Amurka ba har karshen rayuwarsa kuma ba zai samu kudin fansho ba.

Yanzu-yanzu: An tsige Donald Trump matsayin shugaban kasa karo na biyu
Yanzu-yanzu: An tsige Donald Trump matsayin shugaban kasa karo na biyu
Asali: Original

Asali: Legit.ng

Online view pixel