An rufe shafin wasu Magoya bayan Shugaban Amurka Donald Trump a Twitter
- Twitter ta rufe shafukan mutane fiye da 70, 000 a makon da ya gabata
- Ana haramtawa ‘yan gani-kashenin Donald Trump amfani da Twitter
- Magoya bayan Shugaban Amurkan suna yada furogadanda a dandalin
Twitter ya bada sanarwar dakatar da wasu shafuka fiye da 70, 000 da ke da alaka da abin da ya kai ga aika-aika a zauren Capitol a kasar Amurka.
Ana zargin shugaba Donald Trump da tunzura wasu magoya-bayansa da shiga majalisar wakilan Amurka domin nuna adawarsu ga zaben da aka yi a 2020.
A ranar Juma’a, 8 ga watan Junairu, 2020, Twitter ya fara fatattakar rikakkun magoya bayan Donald Trump da ake amfani da su wajen tunzura al’umma.
“Daga Juma’a, an dakatar da sama da shafuka 70, 000 a yunkurin da muke yi na maganin daidaikun mutane da suke amfani da shafuka barkatai.” Inji Twitter.
KU KARANTA: An tsige Trump a Majalisa
“Wadannan shafuka sun labe suna yada karyayyaki, sun dukufa da furofaganda na labaran da ba su tabbata ba a shafin.” Twitter ya cigaba da bayani.
Masu wannan danyen aiki suna ikirarin cewa shugaba Trump ya na yakin boye da gungun Duniya da ke bautar shaidanu da lalata da kananan yara.
Tun bayan da aka samu wasu tsageru sun kutsa majalisar tarayyar Amurka domin hana tantance nasarar Joe Biden, wadannan shafuka suka kara kaimi.
Wannan abu yana cigaba da girgiza Amurka tare da jawowa kasar abin kunya a gaban idon Duniya.
KU KARANTA: Kakakin majalisa Pelosi ta bukaci a tsige Donald Trump
Twitter yace ya bankado kutun-kutun da ake yi na tada tarzoma a kasar Amurka, ta hanyar kai wa majalisa farmaki kafin a rantsar da Joe Biden inji ABC News.
Kamfanonin Facebook da Twitter suna cigaba da yin kaffa-kaffa da nufin hana masu mummunar akida amfani da dandalinsu domin kawo tashin-tashi.
Idan za ku tuna, Twitter ya rufe shafin Trump na tsawon sa'o'i 12, sannan aka goge wasu abubuwa da ya yada, a karshe aka shafe shafin na sa daga dandalin.
A dalilin gudun jawo tarzoma aka rufe shafin Donald Trump mai tarin mabiya kusa miliyan 90.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng