Dattawan Arewa: Babu wani dalili da zai sa Musulmai da Kiristoci yaki da juna

Dattawan Arewa: Babu wani dalili da zai sa Musulmai da Kiristoci yaki da juna

- An bukaci yan Najeriya da su daina yin kalaman da ka iya haddasa tsoro da fusata

- Kungiyar dattawan Arewa ta hannun Dr. Hakeem Baba-Ahmed ce tayi wannan kiran

- A cewar kungiyar, wadanda suka haddasa hakan sun kasance makirai kuma masu mugun nufi

Wasu masu mugun nufi na yin furucin da ka iya tarwatsa kasar a cewar kungiyar dattawan arewa (NEF).

Musamman, kungiyar ta ce mutanen na yin zafafan kalamai a karkashin fakewa da addini.

Ta ce wadannan kalamai na iya haddasa fushi da tsoro a tsakanin al’umma.

Dattawan Arewa: Babu wani dalili da zai sa Musulmai da Kiristoci yaki da juna
Dattawan Arewa: Babu wani dalili da zai sa Musulmai da Kiristoci yaki da juna Hoto: Ripples Nigeria
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: Abubuwan da ya kamata ku sani game da ma'auratan da ake zargin sun yi auren zobe a Kano

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga daraktan labarai na kungiyar, Dr. Hakeem Baba-Ahmed, jaridar This Day ta ruwaito.

Kungiyar ta kuma yi kira ga yan Najeriya a kan su yi hankali da makiran mutane masu haddasa rudani.

“Kungiyar dattawan Arewa (NEF) ta damu a kan kalamai masu sanya damuwa da wasu ke yi ta hanyar fakewa da addini wanda ke haifar da fushi da tsoro a cikin al’umma.”

Da yake ci gaba da magana, ya bukaci gwamnati da ta duba dalilan da za a iya amfani da su wajen haddasa rikicin addini a kasar sannan ta magance su yadda ya kamata.

Ya kara da cewa Musulmai da Kiristoci basu da wasu dalilai na fada da junansu.

A wani labarin, mun ji cewa a yayinda ake tsaka da fafatawa da Bishop Matthew Hassan Kukah, Cif Frank Kokori ya yi kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamna Aminu Tambuwal da su shiga cikin lamarin.

Jigon na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Delta ya yi wannan rokon a wata hira da jaridar Triune a daren ranar Talata, 12 ga watan Janairu.

KU KARANTA KUMA: Rayuwa ba tabbas: Labarin matashin da ya yi hasashen mutuwarsa ya girgiza jama'a

Dattijon ya bukaci Shugaban Najeriya da gwamnan da su dakatar da Khalid Abubakar Aliyu, sakatare-janar na kungiyar JNI daga zuga Musulmai a kan Kukah domin hana rikicin addini.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng