Najeriya yanzu ta zama babbar kango ta yaudara, in ji Bishop Kukah

Najeriya yanzu ta zama babbar kango ta yaudara, in ji Bishop Kukah

- Bishop Mathew Kukah ya sake caccakar mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari

- Malamin ya nanata cewa ba zai yi shuru akan abubuwan da kefaruwa a kasar ba

- Yace duk sadda matsala ta kunno kai dole ne ya fito yayi magana saboda yana da 'yanci

Revd. Matthew Kukah, bishop na Katolika na Sakkwato, ya sake caccakar gwamnatin Najeriya.

Kukah a cikin hudubarsa ta baya-bayan nan ya koka kan yadda Najeriya ta zama kazamar kasa, cike da tarkace, yaudara, karya, cin amana, da kuma rikita-rikita inda duhu ya mamaye komai.

KU KARANTA: Kotun Iraqi ta ba da sammacin damke Donald Trump

Najeriya yanzu ta zama babbar kango ta yaudara, in ji Bishop Kukah
Najeriya yanzu ta zama babbar kango ta yaudara, in ji Bishop Kukah Hoto: The Guardian
Asali: Facebook

Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 6 ga watan Janairu, yayin da yake gabatar da hudubarsa a babban cocin Katolika na St Joseph, Kaduna, a lokacin da ake gudanar da hidimar Archbishop Peter Yariyock Jatau, Archbishop na Kaduna Catholic Diocese.

Shugaban addinin wanda ya kare kansa a sakonsa na Kirsimeti na 2020 wanda ya haifar da martani, ya dage cewa a matsayinsa na malami ba zai iya yin shiru game da abubuwan da ba daidai ba, ya kara da cewa hakkinsa ne ya kula da birnin.

A cewar Kukah, ya kamata ya daga muryarsa a matsayin mai tsaro a duk lokacin da ya hango hatsari a kasar.

Idan za a iya tunawa Kukah ya yi bayani lokacin bikin Kirsimeti wanda ya jawo suka daga magoya bayan Shugaba Buhari.

KU KARANTA: El-Rufai ya saki N100m don yaran da ke fama da tamowa a Kaduna

Malamin siffanta Buhari da nuna kabilanci, ya kara da cewa da a ce dan kudu ne ke mulki a yau, da an yi masa juyin mulki.

Sakon ya girgiza magoya baya da masoya shugaban wadanda suka yi amfani da shafukan sada zumunta inda suka zargi Kukah da ruruta wutar fitina da dumama siyasa.

A wani labarin, Yesufu ta lura cewa dan rajin kare hakkin dan adam, Omoyele Sowore, wanda aka kame a ranar 31 ga Disamba yayin wata zanga-zanga a Abuja, yana da damar yin zanga-zanga a kowace rana matuqar gwamnati na ci gaba da kasancewa "mai gazawa, mara ma'ana, da cin hanci da rashawa, Sahara Reporters ta ruwaito.

Wata mai rajin kare hakkin dan Adam kuma mai daukar nauyin kungiyar 'BringBackOurGirls Movement', Aisha Yesufu, ta caccaki gwamnatin da Shugaba Muhammadu Buhari ke jagoranta, tana mai cewa kasar ta kowa da kowa ce kuma ba wanda ya kamata a kame saboda zanga-zangar lumana.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.