Gwamnatin Kano tace ta gano wasu yaranta da aka sace a Jihar Anambra

Gwamnatin Kano tace ta gano wasu yaranta da aka sace a Jihar Anambra

-Hukumomi sun gano wasu yara da aka sace daga Kano, aka kai su Anambra

-Kwamiti ya dauko hoto da bidiyon wasu yaran da ke gidajen marayu a Kudu

-Wasu iyaye sunyi ikirarin sun gano ‘ya ‘yan na su da aka sace daga hotunan

A ranar Litinin, 11 ga watan Disamba, 2020, gwamnatin jihar Kano ta ce ta gano wasu yara da aka sace a Anambra, Daily Trust ta rahoto wannan.

Kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Muhammad Garba ya shaidawa ‘yan jarida cewa iyayen wasu daga cikin yaran sun gane ‘ya ‘yansu.

Malam Muhammad Garba yace kwamitin da gwamnatin Kano ta kafa domin gano wadanda aka sace mata ya yi dace, ya gano wasu kananan yara.

Kwamishinan yace an yi nasarar gano wadannan yara ne bayan ‘yan kwamitin sun kai ziyara zuwa gidajen marayun da ke Enugu da Anambra.

KU KARANTA: Ganduje zai koma biyan akalla N30, 600 a Kano

“Mun dauki hotuna da bidiyon wadannan yara da nufin gano iyayensu, kuma har wasu iyaye biyar sun gane ‘ya ‘yansu daga wadannan bidiyo.”

Garba ya cigaba da cewa: “Jihar ta na kokarin tabbatar da wannan ikirari na wasu iyayen yaran domin gudun a mika su ga wadanda ba iyayensu ba.”

Kwamsihinan na Kano ya ce gwamnatinsu tana bakin kokarinta na ganin ta ceto wadannan yara, ta hada su da iyayensu ba tare da ta bata lokaci ba.

Ba wannan ne karon farko da aka fara samun labarin yaran da aka sace daga Kano a yankin kudancin Najeriya shekaru bayan an sace su daga gidajensu ba.

KU KARANTA: Dangote ya gangaro daga Attajirin Duniya na 106 a 2021

Gwamnatin Kano tace ta gano wasu yaranta da aka sace a Jihar Anambra
Wasu yaran Kano da aka sace a baya Hoto: www.kanostate.gov.ng
Source: UGC

A dalilin abin da ke faruwa ne gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya kafa kwamiti da zai yi bincike kan yaran da aka rika sace ana saidawa.

Duk a Kano, kun ji cewa hukumar kashe gobara ta Jihar Kano tace mutane uku daga iyalin wani mutum guda sun rasa rayukan su sanadiyar wuta.

Wata gobara da ta tashi ranar Litinin a unguwar Rijiyar Zaki da ke birnin Kano ta yi ta'adi.

A jihar Kwara kuma kun ji cewa an tsinci gawar daraktan ma'aikatar aikin noma, Dr Khalid Ibrahim Ndaman a cikin ofishinsa a garin Ilorin.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel