Gobara ta kashe mutane uku a Kano

Gobara ta kashe mutane uku a Kano

- Wata gobara da ta tashi tsakar dare ta hallaka iyalai uku a garin Kano

- Hukumar kashe gobara tace sai bayan an ceto kuma an garzaya da su asibiti likita ya tabbatar da rasuwar su

- Mai magana da yawun hukumar ya ce su na binciken dalili tashin gobarar

Hukumar kashe gobara ta Jihar Kano ta ce mutane uku daga iyalai guda suka rasa rayukan su sanadiyar wata gobara da ta tashi ranar Litinin a unguwar Rijiyar Zaki da ke karamar hukumar Ungogo a jihar, The Punch ta ruwaito.

Alhaji Saidu Muhammad, mai magana da yawun hukumar kashe gobara ya ce lamarin ya faru da misalin karfe 3:18 na dare kuma gidan ya kone kurmus.

Gobara ta kashe mutane uku a Kano
Gobara ta kashe mutane uku a Kano. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Korona ta yi ajalin likitan Fafaroma Francis

"Mun samu kiran gaggawa daga Malam Salisu Muhammad da misalin 3:18 na dare cewa wuta ta tashi a gidan da ya ke zaune a unguwar su kuma mutum uku suna cikin gidan.

"Samun rahoton mu ke da wuya, mun tura jami'an kai dauki da gaggawa wanda suka isa wajen da misalin 3:22 na daren.

"An ceto cikin mawuyacin hali kuma aka wuce da su asibitin kwararru na Murtala Muhammad inda likita ya tabbatar da mutuwar su," a cewar Muhammad.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kai wa Sanata hari a Osun yayin taro a mazaɓarsa

Ya ce wanda hadarin ya shafa, wanda yan uwa ne su ne, Hauwa Musa, mai shekara 25; Mubarak Musa, 13, sai kuma Salamatu Musa mai shekara 20.

Muhammad ya ce suna binciken dalilin gobarar.

A wani labarin daban, rikici ya kaure a zauren majalisar Jihar kasar Ghana a jiya Laraba 6 ga watan Janairu bayan rushe majalisar kunshi ta bakwai.

A cikin hoton bidiyon da ya karade shafukan dandalin sada zumunta, an gano rikici ne ya kaure tsakanin yan jam'iyyar NPP da NDC kan wacce jam'iyya ne ke da rinjaye kuma wacce zata fitar da sabon Kakakin Majalisa.

Kamar yadda bidiyon ya nuna, wasu daga cikin yan majalisar sun rika kai wa juna hannu sannan wasu suka rika fatali da akwatunan kada kuri'a da ke zauren majalisar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164