Da duminsa: An tsinci gawar daraktan ma'aikatar noma a cikin ofishinsa
- Mutane sun shiga tashin hankali a ma'aikatar noma da habaka karkara dake jihar Kwara a ranar Litinin
- An tsinci gawar wani darekta dake ma'aikatar, Dr Khalid Ibrahim Ndaman, a cikin ofishinsa a kan kujerar
- An shiga ofishin ne inda aka gan shi ya kwantar da kansa a kan teburin ofishinsa a mace babu numfashi
An shiga cikin tashin hankali da rudani da safiyar Litinin a ma'aikatar noma da habaka karkara dake kan titin Jabba a Iloron, lokacin da aka tsinci gawar wani darekta, Dr Khalid Ibrahim Ndaman a ofishinsa.
Vanguard ta tattaro bayanai akan yadda Dr Ndaman ne darekta na bangaren dabbobi a ma'aikatar har zuwa mutuwarsa, inda aka ga gawarsa da safiyar ranar.
An gano cewa daya daga cikin ma'aikatan ya je ofishin domin su tattauna dashi akan wani al'amari na ma'aikatar, a nan ne ya gan shi a mace.
KU KARANTA: Matashiya mai shekaru 18 ta mutu a masaukin bakin gwamnan Yobe, mutum 4 sun shiga hannu
Vanguard ta bayyana yadda aka ganshi ya daura kan shi akan teburin ofishinsa kamar yana hutawa, ashe rai ya yi halinsa.
Wani ma'aikaci ya sanar da Vanguard cewa sai da mutumin yayi ta kwankwasa kofar ofishin Ndaman, bayan ya ji shiru ne ya shiga ofishin ya gan shi matacce.
Kakakin hukumar 'yan sandan jihar Kwara ya tabbatar da aukuwar lamarin.
KU KARANTA: Hotunan direbobin tifa suna toshe babbar hanyar Gusau zuwa Sokoto, sun sanar da dalili
A wani labari na daban, Allah ya karba ran tsohon gwamnan jihar Kano, Aminu Isah Kontagora. An tabbatar da rasuwar tsohon gwamnan bayan sakataren gwamnatin Neja ya bada sanarwar a wata takardar da ya fitar.
Marigayi Aminu Isah Kontagora ya rasu bayan gajeriyar rashin lafiya da yayi fama da ita a garin Abuja.
A lokacin rayuwarsa, ya taba mulkar jihohin Binuwai da Kano a yayin mulkin soja. An haifa marigayin a shekarar 1956 kuma ya mulki jihar Kano daga watan Satumban 1998 zuwa watan Mayun 1999.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng