Da zarar tattalin arziki ya dawo daidai, Ganduje zai koma biyan akalla N30, 600 a Kano

Da zarar tattalin arziki ya dawo daidai, Ganduje zai koma biyan akalla N30, 600 a Kano

- Zaftare albashin da Gwamnatin Jihar Kano ta yi na wani gajeren lokaci ne

- Abdullahi Ganduje yace idan tattalin arziki ya mike, komai zai dawo daidai

- Gwmnan yace rage albashin ya fi a kan ace a sallami wasu ma’aikatan jihar

Gwamnatin jihar Kano a karkashin Abdullahi Umar Ganduje ta tabbatar da cewa ba da wasa ta ke wajen dabbaka tsarin albashi na akalla N30, 000 ba.

Dr. Abdullahi Umar Ganduje yace matakin da aka dauka na rage albashi kamar yadda aka yi a watan Disamban shekarar da ta wuce, ba zai dore ba.

Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa jihar ta fuskanci matsalar karancin kudi sakamakon raguwar abin da ake samu daga kason FAAC da haraji.

Gwamnan ya ce wannan ya jawo aka ragewa ma’aikata albashi, aka dakatar da biyan N30, 000 a matsayin mafi karancin albashin ma’aikacin gwamnati.

KU KARANTA: Ganduje zai koma biyan Ma'aikata N18, 000 duk wata

Mai girma gwamnan yayi wannan bayani ne a wani jawabi da kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Muhammad Garba, ya fitar a ranar Alhamis.

Malam Muhammad Garba ya alakanta rashin biyan cikakken albashin da annobar COVID-19 da kuma matsin tattalin arzikin da Najeriya ta samu kanta.

“Gwamnati ta dauki matakin nan ne a maimakon ta rika biyan rabin albashi, ko a biya sahu-sahu, ko a sallami wasu ma’aikatan kamar yadda wasu ke yi.”

Kwamishinan ya ce: “An dauki irin wannan mataki, irinsu rage alawus din mukarraban ‘yan siyasa lokacin da COVID-19 ta bayyana a watan Maris.”

KU KARANTA: Ma’aikata zasu sa kafar wando daya da Ganduje a kan rage albashi

Da zarar tattalin arziki ya dawo daidai, Ganduje zai koma biyan akalla N30, 600 a Kano
Gwamna Abdullahi Ganduje Hoto: www.rfi.fr/ha/najeriya
Source: UGC

“Da zarar abubuwa sun dawo daidai, gwamnati ba za ta ji kyashin biyan ma’aikata duka albashinsu ba.” Garba ya roki mutane da su daina yada jita-jita.

Hakan na zuwa ne bayan koke-koken da ake yi na cewa an ragewa ma’aikatan jihar Kano albashi.

A dalilin haka aka kai gwamna Abdullahi Ganduje kotu, kuma Alkali ya yanke hukunci cewa gwamnati ba ta damar rage albashin ma’aikatan haka kurum.

Kuna da labarin wasu gwamnoni sun gagara biyan ma’aikata albashin da su ka saba, suna kukan karancin kudi tun daga lokacin da aka shiga annobar COVID-19.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel