Aliko Dangote ya yi gagarumar rashi bayan kamfaninsa ya sullubo a NSE

Aliko Dangote ya yi gagarumar rashi bayan kamfaninsa ya sullubo a NSE

-Aliko Dangote ya rasa kimanin Naira biliyan 350,100,000,000 a makon jiya

-Attajirin da ya mallaki $18.4bn a farkon mako, ya kare da $17.5bn a asusu

-Mai kudin ya sauko a jerin Attajiran Duniya daga na 106, ya koma na 114

Shugaban kamfanin Dangote Industries Limited, Aliko Dangote, ya ga dukiyarsa ta yi kasa a ranar Juma’a, 8 ga watan Junairu, 2020.

Jaridar Punch tace hakan na zuwa ne bayan kasa da kamfanin Dangote ya yi a kasuwar zuba hannun jarin Najeriya watau NSE.

Bloomberg Billionaires Index wanda ta ke tattara alkaluman attajiran Duniya ta nuna Alhaji Aliko Dangote ya rasa Dala miliyan 900.

Dangote wanda ya mallaki $18.4bn a ranar Alhamis, ya wayi gari ranar Juma’a da $17.5bn a asusunsa.

KU KARANTA: Dangote da sauran manyan Attajiran da suka fi kowa arziki a Afirka

Da wannan canji da aka samu, Dangote wanda shi ne attajiri na 106 a kaf Duniya kafin yanzu, ya koma na 114 a sabon jerin da aka fitar.

Bayan ya samu karin Dala miliyan 600 a farkon kwanakin 2021, Aliko Dangote ya gamu da wannan babbar asarar cikin sa’o’i 24.

Abin da hamshakin Attajirin Nahiyar Afrikan ya rasa a wannan takaitaccen lokaci a darajar kudin Najeriya, ya haura Naira biliyan 350.

A tsakiyar Disamban 2020, dukiyar Dangote ta yi wani tashi daga Dala biliyan 15.5 zuwa dala 17.8, sama da Naira tiriliyan shida kenan.

KU KARANTA: Dangote, BUA, da wasu 'Yan Najeriya 2 sun shiga jerin Forbes a 2020

Aliko Dangote ya yi gagarumar rashi bayan kamfaninsa ya sullubo a NSE
Aliko Dangote Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Har yanzu, Dangote ne kadai mutumin Najeriya da ya iya shiga jerin Attajirai 500 na farko da ake da su a Duniya, na farko a fadin Afrika.

A shekarun baya ne muka kawo maku wani takaitaccen tarihin kasuwanci da rayuwar ‘Dan kasuwan Duniya, Alhaji Aliko Dangote.

Kamar yadda kuka ji a wancan lokaci,Aan haifi Aliko Dangote ne cikin Dangin Attajirin nan na kasar Kano, Alhaji Alhassan Dantata.

Mahaifiyar Dangote Hajiya Mariya Sanusi ‘Diya ce wajen tsohon mai kudin Yankin Afrika.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng