Ya kamata a zabe mai zuwa, mulki ya koma Kudu maso yamma inji YPM da Afenifere

Ya kamata a zabe mai zuwa, mulki ya koma Kudu maso yamma inji YPM da Afenifere

- Kungiyar Afenifere ta bukaci a bar Bayarabe ya zama Shugaban kasa a 2023

- Afenifere ta na so jam’iyyar APC ta ba mutumin Kudu maso yamma takara

- Ita ma kungiyar PYM ta na ganin lokaci ya yi da Yarbawa za su karbi kasar

Kungiyar Afenifere ta sha alwashin cewa mutumin bangaren Kudu maso yammacin Najeriya ne zai zama shugaban kasa bayan Muhammadu Buhari.

Afenifere da wata kungiyar matasa ta Yoruba Patriots Movement, suna ganin cewa 2023 lokaci ne da Bayarabe zai fito neman takarar shugaban Najeriya.

Jaridar The Nation ta fitar da rahoto cewa wadannan kungiyoyi sun ba jam’iyyar APC shawara, ta girmama yarjejeniyar da aka yi kafin babban zaben 2015.

Kungiyoyin yarbawan su ka ce idan aka karrama wannan yarjeniya ne za a tabbatar da adalci.

KU KARANTA: Ana ta sauya-sheka a Majalisa saboda 2023

Shugaban kungiyar YPM na kasa, Oladosu Oladipo, ya fito gaban Duniya ya na cewa ba su yarda da wani abu ba face Bayarabe ya karbi mulkin Najeriya.

Mista Oladosu Oladipo ya yi wannan bayani ne a ranar Laraba, 7 ga watan Junairu, 2021 wajen wani taro da aka shirya a Ibadan a kan makomar Yarbawa.

An yi wa wannan gagarumin taro ne da taken: “Kasar Yarbawa, jiya yau da gobe”, inda bayan an kammala zaman, Oladipo ya zanta da manema labarai.

Sakataren kungiyar Afenifere a karkashin jagorancin Sanata Biyi Durojaiye da Bayo Aina sun ce APC mai mulki ce kawai za ta iya ba Bayarabe tikitinta.

KU KARANTA: Na cika alkawarin da na yi wa nakasassu - Buhari

Ya kamata a zabe mai zuwa, mulki ya koma Kudu maso yamma inji YPM da Afenifere
Taron manyan APC Hoto: Twitter Daga: @MBuhari
Source: Twitter

Har aka tashi taron, kungiyoyin ba su fadi yarjejeniyar da aka yi a 2015 ba, sannan ba su kama sunan wani ‘dan siyasar da ake ganin ya dace da takara ba.

A makon nan kun ji cewa tseren samun tikitin takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC a zabe mai zuwa ya jawo rigima a jam’iyyar APC mai mulki a jihar Ekiti.

Ana zargin cewa Bola Tinubu da gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi su na neman kujerar Buhari.

A dailin hakan, an ja layi tsakanin yaran Bola Tinubu da masu goyon bayan gwamna Fayemi. Dukkansu biyu sun fito ne daga yankin Kudu maso yamma.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel