Yamutsi a Jam’iyyar APC a kan niyyar takarar Bola Tinubu da Kayode Fayemi

Yamutsi a Jam’iyyar APC a kan niyyar takarar Bola Tinubu da Kayode Fayemi

- Ana tunanin Bola Tinubu da Kayode Fayemi za su yi takara a zabe mai zuwa

- Jiga-jigan na jam’iyyar APC suna hangen kujerar shugabancin Najeriya a 2023

- Ba a ga maciji tsakanin tsohon gwamnan Legas Tinubu da Dr. Kayode Fayemi

Tun 2018 ake rigingimu iri-iri a jam’iyyar APC a jihar Ekiti. Jaridar Punch ta alakanta wannan sabani da kudirin Kayode Fayemi da Asiwaju Bola Tinubu.

Jam’iyyar APC ta rabu gida biyu a Ekiti tsakanin gwamna Kayode Fayemi da mutanensa da bangaren irinsu Sanata Anthony Adeniyi da Babafemi Ojudu.

Masu hasashe, nazari da fashin bakin siyasa a Najeriya suna ganin cewa hangen takarar 2023 ya kawo rashin jituwa tsakanin Kayode Fayemi da Bola Tinubu.

Duk da babu wani cikin wannan ‘yan siyasa da ya fito fili yace zai nemi takara a 2023, amma alamu suna nuna cewa mutanensu na yi masu yaki tun yanzu.

KU KARANTA: Buhari ya gana da manyan jiga-jigan APC a fadar shugaban kasa

Jagoran APC a Ekiti, Ade Ajayi, bai boye wannan magana ba inda kwanakin baya ya fito yana cewa za su nemi Fayemi ya fito shugaban kasa a zaben 2023.

“Ko da gwamna Fayemi bai ce ya na son takara ba, za mu tursasa shi ya shiga cikin masu neman kujerar, saboda sanin aikinsa da biyayya ga APC” inji Ajayi.

Wannan magana ta batawa wasu ‘yan bangaren jam’iyyar rai, wanda a ra’ayinsu ba gwamnan na Ekiti ne ya kamata ya nemi kujerar shugaban kasa a APC ba.

Mutanen tsohon gwamnan Legas, Bola Tinubu ne su ke kokarin watsi da maganar takarar Fayemi.

KU KARANTA: 'Ya 'yan PDP sun tattara sun koma jam'iyyar APC a Zamfara

Yamutsi a Jam’iyyar APC a kan niyyar takarar Bola Tinubu da Kayode Fayemi
Taron majalisar kolin Jam’iyyar APC Hoto: BBC Daga: www.bbc.com/pidgin/tori-53180988
Asali: UGC

Hon. Karounwi Oladapo na majalisar dokokin Ekiti ya caccaki yaran tsohon gwamnan, ya ce ‘yan tara-gutsa ne kurum su ke tare da Bola Tinubu a jam’iyyar APC.

Gabanin zaben ranar 16 ga watan Janairu 2020 a jihar Kano, an yi fatali da wasu 'yan takara.

Idan ku na biye da mu, kun san cewa ana shirin zaben kananan hukumomin jihar Kano.

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta a jihar Kano, Garba Ibrahim Sheka ya ce an watsi da wasu 'yan takara da su ka fadi gwajin amfani da miyagun kwayoyi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng