Na cika alkawarin da na dauka wa nakasassun yan Najeriya, shugaba Buhari

Na cika alkawarin da na dauka wa nakasassun yan Najeriya, shugaba Buhari

- Buhari ya cika alkawarinsa ga al'ummar nakasassun Najeriya, a cewarsa

- Hajiya Sadiya Umar Farouq ta kai nakasassu fadar shugaba kasa

Shugaba Muhammadu ya bayyana cewa lallai ya cika alkawarin da yayi wa al'ummar nakasassun Najeriya ta hanyar kafa musu sabuwar ma'aikata.

Buhari ya bayyana hakan ne yayinda ya karbi bakuncin mambobin hukumar nakasassun Najeriya.

Mambobin hukumar sun kaiwa shugaba Buhari ziyara ne ranar Alhamis, 7 ga watan Junairu, 2021, karkashin jagorancin ministar walwala da jinkan jama'a, Hajiya Sadiya Umar Farouq.

A jawabin da yayi a shafinsa na Tuwita @Mbuhari da yammacin Alhamis, Buhari ya bayyana cewa ya rattafa hannu kan dokar jin dadin nakasassu a Najeriya.

Hakazalika ya kaddamar da hukumar kula da nakasassu domin cigaba da aiki.

"Ina farin cikin cika alkawarin da na yiwa al'ummar mutane masu nakasa, ta hanyar rattaba hannu kan dokar nakasassu," Buhari yace.

"Hakazalika mun rantsar da mambobin hukumar mutane masu nakasa domin cigaba da aikin da kuma wanzar da manufarmu."

KU KARANTA: Chasun Badala: Kaduna ta gurfanar da kakakin PDP tare da wasu da laifin yunkurin aikata badala

Na cika alkawarin da na dauka wa nakasassun yan Najeriya, shugaba Buhari
Na cika alkawarin da na dauka wa nakasassun yan Najeriya, shugaba Buhari Hoto: @Buharisallau1
Asali: Twitter

KU DUBA: Najeriya yanzu ta zama babbar kango ta yaudara, in ji Bishop Kukah

Na cika alkawarin da na dauka wa nakasassun yan Najeriya, shugaba Buhari
Na cika alkawarin da na dauka wa nakasassun yan Najeriya, shugaba Buhari Hoto: @Buharisallau1
Asali: Twitter

A wani labarin kuwa, duk da rashin amincewar masu hannun jari, gwamnatin tarayya na shirin aron kudaden yan Najeriyan da ke asusun da aka dade ba'a waiwayesu ba, da kuma kudaden masu hannun jarin da aka dade ba'a bibiya ba.

Gwamnatin zata samu daman yin hakan ne bisa dokar kudin 2020 da shugaba Muhammadu Buhari ya rattafa hannu.

Karkashin sashe na 12 na dokar, an bayyana cewa za'a iya aron kudaden masu hannun jarin da ajiyan na mutanen wanda suka kai shekaru 6 ba'a waiwaya ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng