2023: Guguwar sauyin sheka ta sake dawowa majalisar wakilai

2023: Guguwar sauyin sheka ta sake dawowa majalisar wakilai

- Ficewar wasu mambobin majalisar wakilai daga Jam'iyyar PDP zuwa APC ta haddasa cece-kuce a zauren majalisa

- Wani rahoto ya gano cewa akwai yiwuwar samun karin wasu mambobin majalisar da zasu koma APC a cikin satin nan

- Sauyin shekar mambobin ba zai rasa nasaba da shirye-shiryen zaben shekarar 2023 ba

Idan za'a iya tunawa, a cikin shekarar da ta gabata, 2020, an samu 'yan siyasa, musamman a cikin zauren majalisar wakilai ta tarayya, da suka canja sheka daga PDP zuwa jam'iyyar APC ko kuma daga APC zuwa PDP.

Ko a ranar 15 ga watan Disamba, 2020, 'yan majalisar wakilai biyu, Hon. Ali Datti Yako, daga Kano, da kuma Danjuma Shittu daga Taraba, sun fice daga asalin jam'iyyarsu, PDP, zuwa jam'iyya mai mulki ta APC.

Shugaban majalisar, Femi Gbajabiamila, ne ya karanta wasikar ficewar tasu lamarin da ya janyo hayaniya a majalisar daga ya'yan jam'iyyar PDP wadanda suka nemi a bayyana kujerun mambobin a matsayin wacce bata da wakili a zauren majalisar.

KARANTA: Sanata Shehu Sani: Abubuwa 10 da duk mai sha'awa ko burin shiga siyasa a Nigeria ya kamata ya sani

Sai dai shugaban majalisar, Femi Gbajabiamila, ya ce kotu ce kaɗai ke da hurumin yin hakan.

2023: Guguwar sauyin sheka ta sake dawowa majalisar wakilai
2023: Guguwar sauyin sheka ta sake dawowa majalisar wakilai @HouseNGR
Asali: Twitter

Ya kuma tuna musu a baya cewa tsohon shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, da na wakilai, Yakubu Dogara, sun fice daga APC, sun koma PDP.

KARANTA: Fadar shugaban kasa ta radawa jam'iyyar PDP sabon suna na wulakanci

"Kun nemi da a ayyana kujerar shugaban majalisar dattijai da kakakin majalisar wakilai kujerun da ba su da wakilci lokacin da suka fice daga APC?

"Shin ni ko kotu ne ke da damar fassara kundin tsarin mulki? Ni ba kotu ba ne" in ji kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila.

Jaridar Vanguard ta gano cewa akwai alamun samun ƙaruwar waɗanda za su sauya sheka zuwa jam'iyyar APC a cikin zauren Majalisar daga jihar Abia a wannan satin.

A baya Legit.ng ta rawaito cewa Malam Ibrahim Shekarau, tsohon gwamnan jihar Kano, ya ce babu gurbin tsarin kama-kama a mulkin kasa a cikin kundin tsarin mulkin jam'iyyar APC.

Tsohon gwamnan kuma sanatan Kano ta tsakiya ya ce cancanta ce ya kamata ta zama abar dubawa a zaben gaba.

Shekarau ya yi tsokaci akan alakar da ke tsakaninsa da gwaman Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje da tsohon gwamna Kwankwaso.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng