Donald Trump ya ce za a gabatar da hujjoji yayin da za a tantance kuri’un zabe

Donald Trump ya ce za a gabatar da hujjoji yayin da za a tantance kuri’un zabe

- Donald Trump ya dage a kan sai ya zarce a kan kujerar shugaban Amurka

- Shugaban kasar Amurkan ya yi jawabi a Twitter, ya na cewa an yi magudi

- Trump ya ce za a gabatar da wasu hujjoji da ke nuna an murde zaben 2020

Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya na nan a kan bakarsa na cewa shi ne wanda ya lashe zaben da aka gudanar a karshen shekarar 2020.

Donald Trump ya rantse cewa shi ne ainihin zababben shugaban Amurka, duk da hukuma ta tabbatar da Joe Biden ya lallasa shi a zaben bara.

A wata magana da shugaban Amurkan ya yi a shafinsa na Twitter, Trump ya bayyana cewa zai gabatar da hujjojin da za su tabbatar da gaskiyarsa.

Donald Trump mai shekara 74 a Duniya ya ce ya lashe zaben na 2020 da gagarumar nasara.

KU KARANTA: Kotun koli ta yi watsi da karar Donald Trump na kalubalantar zabe

Da yake magana a ranar Juma’a 1 ga watan Junairu, 2020, shugaban kasar mai jiran barin gado ya yi wa dinbin masoyansa albishir da cewa zai fasa kwai.

“Za a gabatar da hujjoji rututu a ranar 6 (na watan Junairu 2020). Mun samu gagarumar nasara.”

Da yake karin bayani a ranar Lahadi, Trump ya tabbatar da cewa zai halarci gangamin da za a shirya domin nuna rashin ingancin zaben da aka yi.

Wasu daga cikin ‘yan majalisar tarayyar Amurka irinsu Sanata Josh Hawley mai wakiltar mazabar Missouri sun ce ba su yarda da nagartar zaben ba.

KU KARANTA: Trump ya fasa kai wa Iran hari

Donald Trump ya ce za a gabatar da hujjoji yayin da za a tantance kuri’un zabe
Shugaba Donald Trump Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ko da Trump ya ke wannan magana a shafin na sa, Twitter sun ja hankalin jama’a cewa babu tabbas a game da ikirarin da shugaban Amurkan ya ke yi.

A baya kun ji cewa da alamu Donald Trump ya hakura da kashin da ya sha. Rahotanni sun ce shugaba Trump ya na la’akari da sake fitowa takara a 2024.

Idan shugaba Trump bai samu tazarce kamar yadda ya ke nema ta kafar kotu ba, zai hakura ya mikawa Joe Biden mulki, ya sake fitowa takara a zabe mai zuwa.

Tsofaffin Hadiman shugaban kasar sun bijiro masa da batun ya bada mulki, ya tari gaba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Nigeria

Online view pixel