Da duminsa: Kotun koli ta yi watsi da karar Donald Trump na kalubalantar sakamakon zabe

Da duminsa: Kotun koli ta yi watsi da karar Donald Trump na kalubalantar sakamakon zabe

- Kotun Kolin Amurka ta yanke hukunci kan karar da ke kalubaantar sakamakon zaben shugaban kasa

- Kotun a shari'ar da ta yanke ta bayyana dalilin da yasa tayi watsi da karar Donald Trump

- Har yanzu dai ba'a sani ko Trump zai cigaba da yunkurin kalubalantar sakamakon zaben ba

Yunkurin Donald Trump na sauya sakamakon zaben shugaban Amurka ya samun cikas yayinda kotun koli tayi watsi da kokarin ragewa Joe Biden milioyin kuri'u a jihohin da ya lashe.

A cewar CNN, kotun a ranar Juma'a, 11 ga Disamba, ta yanke cewa karar da babban lauyan jihar Texas, Ken Paxton, ya shigar a madadin Trump bai da kamshin gaskiya a shari'a.

Sky News ta ruwaito cewa Trump ya tuhumi sakamakon zaben jihohin Georgia, Michigan, Pennsylvania da Wisconsin, da aka zabu Biden.

Gwamnotin jihohi 18 a Amurka da akalla yan majalisun jam'iyyar Republican 100 sun goyi bayan karar.

Amma kotun kolin ta ce ba za iya kansile miliyoyin kuri'un ba.

KU KARANTA: Yan ta'adda sun yi awon gaba da Ango da abokinsa bayan daurin aure

Da duminsa: Kotun koli ta yi watsi da karar Donald Trump na kalubalantar sakamakon zabe
Da duminsa: Kotun koli ta yi watsi da karar Donald Trump na kalubalantar sakamakon zabe
Asali: Getty Images

KU KARANTA: Harin Kankara: Gwamna Masari ya kulle dukkan makarantun kwana a jihar Katsina

A tarihin Amurka, shugabannin kasa suna samun nasarar tazarce bayan karewar wa'adinsu na farko saboda irin ayyukan da suka yi.

Amma ba haka ya faru da Donald Trump ba saboda lokacin da ya kaddamar yakin neman zabensa a 2019, maki 43% kadai ya samu, cewar Gallup.

Trump ya samu nasarar lashe zabe a jihohi 23 yayinda Biden ya lashe a jihohi 27.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng