Trump da ya fadi dalilin sa na fasa kaiwa Iran hari

Trump da ya fadi dalilin sa na fasa kaiwa Iran hari

Shugaba Donald Trump na Amurka, a ranar Juma'a ya ce ya fasa kai kai wa kasar Iran hari ne bayan ya yi la'akari da mutanen da za su iya mutuwa a dalilin harin.

Mista Trump ya fusata ne tun bayan da Iran ta harbe jirgin leken asirin amurka mara matuki a ranar Alhamis. Kasashen biyu basu cimma matsaya kan matsayin jirgin ba a lokacin da aka harbe shi.

Iran ta ce jirgin ya shigo cikin iyakokin tekun ta a amma Amurka ta musanta hakan inda ta ce jirgin ya tsaya ne a wani wuri da ke da nisan mil 21 daga iyakar Iran.

DUBA WANNAN: Da duminsa: An kama kwararen mayaki na kasa da kasa cikin 'yan Boko Haram a Borno

Mr Trump ya bawa sojojin Amurka umurnin kai harin gaggawa kan wasu muhimman gine-ginen sojojin Iran a daren Alhamis amma daga bisani ya fasa kai harin kamar yadda New York Times ta ruwaito a daren Alhamis.

Shugaban na Amurka ya bayyana cewa ya bayar da umurnin kai harin amma ya canja ra'ayinsa bayan shugabanin sojoji sun fada masa adadin mutanen da za su iya mutuwa sakamakon harin.

"Mun shirya tsaf domin kai harin ramuwar gayya kan wasu wurare uku amma na tambaya mutane nawa za su mutu, sai wani Janar ya fada min mutane 150. Mintuna 10 kafin harin na bayar da umurnin a fasa." kamar yadda Trump ya rubuta a Twitter.

Mista Trump ya ce zai kara tsaurara matakan ladabtarwa kan Iran saboda hana kasar samun damar mallakar makamai masu linzami kuma sai kai batun gaban Majalisar Dinkin Duniya.

Mahukuntan Iran sun ce harbe jirgin da su kayi ba laifi bane saboda ya shigo kasarsu ba tare da izinin ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel