Aregbesola: Har gobe babu wanda zai kawowa Najeriya haramtattun kayan waje

Aregbesola: Har gobe babu wanda zai kawowa Najeriya haramtattun kayan waje

- Gwamnatin Najeriya ta ce bude iyakoki ba zai bada damar shigo da shinkafa ba

- Rauf Aregbesola yace sam ba za a bari a shigo da kayan waje da aka haramta ba

- Ministan yace an kafa na’urar MINARS a kan iyakokin tudu saboda fasa-kauri

Ministan harkokin cikin-gida, Rauf Aregbesola, yace duk da bude iyakokin tudu da aka fara yi, babu maganar shigo da shinkafa daga ketare.

Jaridar Punch, ta rahoto Ministan yana wannan bayani a ranar Asabar lokacin da ya gana da ‘yan jarida.

Rauf Aregbesola da ya ke magana a garin Ilesa, ya ce akwai fasahohin da za su sa a gano shinkafa duk yadda aka yi kokarin shigo da ita a boye.

“Mun kawo wata fasaha wanda ake kira MINDARS, a iyakoki hudu da mu ka bude. MIDARS zai yi wa duk wanda ya shigo cikin Najeriya rajista.”

Kara karanta wannan

Wasu Shugabannin PDP na Neman Tada Rikici, Sun ce An Ware Su a Yakin Zaben Atiku

KU KARANTA: Abin da ya sa Gwamnatin Buhari ta amince da bude iyakoki

Yace: “Idan MINDARS ta yi wa mutum rajista, har abada an san da zaman shi, don haka babu wanda ya isa ya shigo Najeriya ba tare da an gane ba.”

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mai girma Ministan ya bayyana cewa an bude iyakokin tudun ne domin mutane su shigo cikin kasar, sannan a rika cinikin kayan Afrika ta yamma.

“Kayan da mu ka hana shigo da su sune na waje. Ana cin shinkafar waje ne a Najeriya da kasar Afrika ta yamma kawai..” Ministan ya yi karin-haske.

“Bude iyakokin bai bada damar shigo da kayan da aka haramta ba, irinsu tsuntsaye, shinkafa da kwayoyi, makamai, makudan kudi ba.” Inji Aregbesola.

KU KARANTA: Kalaman Shettima sun jawo masa matsala, an zarge shi da kokarin kifar da Buhari

Kara karanta wannan

APC ta Fallasa Abinda Ya Kawo Hargitsi A Gangamin PDP na Kaduna

Aregbesola: Har gobe babu wanda zai kawowa Najeriya haramtattun kayan waje
Rauf Ogbeni Aregbesola Hoto: twitter.com/raufaregbesola
Asali: Twitter

Tsohon gwamnan ya kuma musanya rade-radin cewa ya samu sabani da gwamnan jihar Osun mai-ci, Adegboyega Oyetola, ganin sun yi wani taron sulhu.

Bayan watanni 16 da garkame Najeriya, kun ji an bude iyakokin tudu hudu da ke cikin kasar.

Hakan na zuwa ne bayan an zargi hukumar shiga da fice da kin bin umurnin da Mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada kwanan nan.

Mai magana da yawun hukumar shige-da-fice, Sunday James, ya musanta wannan zargi, ya ce sun bi umurnin gwamnatin tarayya na bude iyakokin.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Kara karanta wannan

Ziyarar da Peter Obi Ya Kai wa Dr. Ahmad Gumi ta Jawo Masa Bakin jinin Magoya baya

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng