Annobar COVID-19, da matsin tattali suka jawo bude iyakokin Najeriya a 2020

Annobar COVID-19, da matsin tattali suka jawo bude iyakokin Najeriya a 2020

- Tun shekarar 2019 aka rufe iyakokin kasan Najeriya har zuwa makon jiya

- Matsin tattalin arzikin da aka shiga ya taimaka wajen sake bude iyakokin

- Bayan haka, annobar COVID-19 ta na cikin abin da ya sa aka sake shawara

Jaridar Vanguard ta bi diddiki ta binciko dalilan da su ka sa gwamnatin tarayya ta bude iyakokin kan tudu bayan an rufe su tun cikin shekarar 2019.

Rahoton da jaridar ta fitar a ranar 21 ga watan Disamba, 2020, ya bayyana cewa annobar COVID-19 da ta barke ta taka rawar gani wajen wannan mataki.

Garkame iyakokin da gwamnatin Muhammadu Buhari ta yi, ya jefa ‘yan kasuwa da masu hannun jari da kuma talakan Najeriya a cikin halin wayyo Allah.

Wata majiya mai karfi a fadar shugaban kasa da ta yi magana da jaridar ta ce wahalar da Bayin Allah suka shiga ya sa gwamnati ta bude iyakokin tudun.

KU KARANTA: Buhari: A bude iyakokin Illela, Seme, Mfun da M/Gatari

Bayan haka, an shawo kan shugaban kasa cewa gwamnatin tarayya tayi nasarar dakile ta’adin da ake yi ta bakin iyakokin, don haka aka sake bude iyakokin.

Wata nasara da aka samu a tsawon wannan lokaci shi ne Najeriya ta gargadi kasashen da take makwabtaka da su cewa ba za ta yarda da abin da ke faruwa ba.

Ana zargin kasashen da ke kusa da Najeriya da kawowa tattalin kasar cikas ta matsalar fasa-kauri.

A rahoton da gwamnati ta fitar, ta bayyana yadda kasuwancin jama’a ya tagayyara a sakamakon rufe iyakokin, wanda hakan ya hana shiga da fitar kaya da tsada.

KU KARANTA: Za mu bude iyakoki - Minista

Annobar COVID-19, da matsin tattali suka jawo bude iyakokin Najeriya a 2020
Ministoci a taron FEC Hoto Twitter/NgrPresident
Asali: Twitter

Wani dalili da ya jawo hakan shi ne tulin kaya da akeda su a Najeriya da ake bukatar a fitar da su waje, wanda yin hakan zai kawo kudin shiga da samar da abin yi.

Haka zalika Gwamnatin tarayya ta yi la’akari da cewa ta shiga yarjejeniyar AfCFTA da ETLS wanda ya bada damar a rika cinikiyya tsakanin kasasshen Afrika.

Kwanaki mun kawo maku wasu hanyoyi da sake bude iyakokin tudu zai taba talaka da tattalin arzikin kasa kamar yadda wasu masana suka fara sharhi a Najeriya.

Rufe iyakokin ya haddasa masifaffen tashin farashin kaya, ana sa ran yanzu za a samu sa'ida.

Masana sun bayyana cewa rufe iyakokin ya hana satar man Najeriya zuwa ketare, amma kuma ya kashe ‘yan kasuwan gida a dalilin rashin taimakawa kamfanoni.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel