Mun bi umurnin Buhari, mun bude iyakoki: Hukumar shiga da fice
- Bayan watanni 16 da kulle iyakokin Najeriya, an bude guda hudu
- An zargi hukumar shiga da fice da kin bin umurnin Buhari bayan kwana biyu da yin ta
- Mai magana da yawun hukumar ta musanta wannan zargi
Hukumar shiga da ficen Najeriya ta ce ta bi umurnin gwamnatin tarayya na bude iyakokin Najeriya.
Hakan na kunshe cikin jawabin da jami'in hulda da jama'a na hukumar, Sunday James, ya rattafa hannu kuma ya aikewa yan jaridar ranar Juma'a a Abuja.
"Bisa ga umurnin da gwamnatin tarayya ta bada, an bude iyakokin Najeriya," jawabin yace.
Jawabin ya ce iyakokin sune Seme a kudu maso yamma, Illela a Arewa maso yamma, Maigatari a Arewa maso yamma da Mfum a kudu maso kudu.
Ya ce an bude iyakokin tun bayan da aka rufe a ranar 20 ga Agusta, 2019.
A cewarsa, kwantrola janar na hukumar ya umurci manyan jami'an dake kula da iyakokin su cire dukkan takunkumin da suka sanya a iyakokin.
KU KARANTA: Pantami ya bada umurnin rufe layukan marasa lambar katin zama dan kasa
KU DUBA: Muna da tabbacin Buhari zai kawo karshen rashin tsaro, Gwamnonin APC
A ranar 16 ga Disamba, shugaba Buhari ya bada umurnin bude iyakoki hudu da suka raba Najeriya da makwabtanta.
Iyakokin guda hudu da za'a bude sune kamar haka: Illela a Jihar Sokoto, Maigatari a jihar Jigawa, dukkansu a arewacin Nigeria.
Sai kuma iyakar Seme da ke Jihar Legas, yankin kudu maso yamma, da iyakar Mfun da ke yankin kudu maso kudu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng