Kungiya tana so a kama Kashim Shettima, ta zarge shi da neman hambarar da Gwamnati

Kungiya tana so a kama Kashim Shettima, ta zarge shi da neman hambarar da Gwamnati

- CBSG ta yi kaca-kaca da Kashim Shettima na cewa a canza Shugabannin Soji

- Kungiyar ta kai ga zargin Sanatan na APC da shiryawa gwamnati juyin-mulki

- Wannan kungiya tace tsohon Gwamnan yana da hannu a matsalar rashin tsaro

Wata kungiya ta abokai da kuma magoya bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari (CBSF) ta dura kan tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima.

Wannan kungiya ta CBSF tana zargin Sanata Kashim Shettima da laifin kitsa juyin-mulki a Najeriya, ta yadda za a hambarar da Muhammadu Buhari.

Jaridar Blueprint ce ta fitar da wannan rahoto a ranar Alhamis, 17 ga watan Disamba, 2020.

Kamar yadda mu ka samu labari daga rahoton, gamayyar wannan kungiya ta CBSF, ta na ikirarin cewa ta na tare ne da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

KU KARANTA: An kai Buhari kotu a kan wa'adin Hafsun tsaro

CBSF ta bukaci a cafke Kashim Shettimam sannan a gurfanar da shi a kotu bisa wannan laifi da kungiyar ba ta iya bada hujjar dake nuna Sanatan ya aikata ba.

A cewar kungiyar magoya bayan shugaban kasar, Shettima ya kauce hanya da wasu kalamansa.

Shugaban CBSF, Shamsudeen Abu, ya fitar da wannan jawabi, har ya zargi Shetimma da hannu a matsalar rashin tsaro da ake fama da ita a Arewa maso gabas.

Dr. Abu ya ce a lokacin da Shettima ya yi mulki a Borno, bai yi wani abin kwarai na kawo zaman lafiya ba, a karshe ya tattara ya tsere majalisar dattawa a 2019.

KU KARANTA: 2023: APC ta zabi ‘Yan siyasan da za su karbo yankin Jonathan

Kungiya tana so a kama Kashim Shettima, ta zarge shi da neman hambarar da Gwamnati
Kashim Shettima Hoto: Borno state governor Kashim Shettima
Source: Facebook

Kalaman da kungiyar ta ke nufi su ne kiran da Sanata Shettima ya yi na cewa a sauke hafsun sojoji a dalilin matsalar da ake yawan samu yanzu a harkar tsaro.

Idan za ku tuna, Sanatan Borno ta tsakiyar ya bayyana dalilai, wanda a cewarsa sun isa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada wasu shugabannin sojoji.

A wata hira da aka yi da Kashim Shettima yace dole su fadawa shugaban kasa gaskiya duk da cewa suna tare da shi, yace hafsun soji sun dade a kan kujera.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel