Rashin tsaro: Manyan hafsoshin tsaro ya dace su amsa kirar majalisa ba Buhari ba, jigon APC
- Jigo a APC Farouq Aliyu ya bayyana cewa bai kamata Buhari ya amsa gayyatar majalisar tarayya ba dangane da matsalar tsaro
- Ya ce idan zai baiwa shugaban shawara zai ce masa kar yaje, illa dai ya tura manyan hafsoshin tsaro
- Ya kuma bayyana cewa Buhari ba mai son yawan surutu ba ne amma kasar na da baiwar wanda ke da azanci a magana
Wani jigo a jam'iyyar APC, Farouq Aliyu, ya ce ba shugaba Buhari ba ne ya kamata ya amsa gayyatar majalisar tarayya ba dangane da matsalar tsaro a kasar nan.
Da ya ke zantawa da gidan talabijin din Channel ranar Laraba a Abuja, Aliyu ya bayyana cewa manyan hafsoshin tsaro ne ya kamata su bayyana a gaban yan majalisar don yi wa yan Najeriya jawabi kan irin matakan da su ke bi don kawo karshen matsalar tsaro.
DUBA WANNAN: Mafi yawancin 'yan matan da ake latsa wa a manyan makarantu daƙiƙai ne, in ji Gwamna Ayade
"Idan zan ba wa shugaban kasa shawara, zan ce ma sa kar ya je. Zan ce masa ya tura hafsoshin tsaro don sai an fi samun bayanai muhimmai a wajen su," a cewar sa.
"A matsayina na tsohon shugaban marasa rinjaye a majalisa, ba na tunanin ya kamata shugaban ya je. Ba a irin wannan lokacin da komai ya yi tsauri ba, kasar ta na fama da matsaloli. Shugaban zai bayyana ne gaban majalisa don bayanin matakin da gwamnati ke dauka?
"Zai je ne saboda mahawara? Ko shugaban majalisa ba zai ce ran shugaban kasa ko jam'iyyarsa bai baci ba."
KU KARANTA: Yan sanda sun ce sun kashe kasurgumin dan bindiga a Niger
Da ya ke kare ikirarin sa kan cewa kar Buhari ya amsa gayyatar majalisar kan matsalar tsaro, tsohon shugaban marasa rinjayen ya ce shugaban kasar ba mai yawan magana bane.
Ya ce shugaban kasar bai fiye son magana ba, ya ce kasar ta na da baiwar mutane da suka iya magana.
A wani labarin daban, Shugaba Muhammadu Buhari ya sauke shugaban hukumar daukan ma'aikata, Dakta Nasiru Mohammed Ladan Argungu daga mukaminsa.
Sanarwar saukewar na kunshe ne cikin wata wallafa da babban mataimakin shugaban kasa a bangaren watsa labarai, Mallam Garba Shehu ya fitar a ranar Talata kamar yadda The Punch ta ruwaito.
Sanarwar ta ce Buhari ya umurci karamin ministan Kwadago da Ayyuka, Festus Keyamo, SAN, ya nada shugaban riko daga cikin manyan direktocin hukumar don maye gurbin Argungu a yanzu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng