Hotunan kamun auren jarumin Kannywood, Nuhu Abdullahi

Hotunan kamun auren jarumin Kannywood, Nuhu Abdullahi

- An fara shagulgulan bikin shahararren jarumin Kannywood, Nuhu Abdullahi

- Zuwa yanzu an yi wasan kwallo na bikin da kuma kamun amarya

- A yau Juma’a, 4 ga watan Disamba ne za a daura aure tsakanin Nuhu da amaryarsa Jamila

Alkawari dai na shirin cika tsakanin shahararren jarumin nan na masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Nuhu Abdullahi da sahibarsa, Jamila Abdulnasir.

Tuni dai aka fara shagulgula na bikin inda a ranar Laraba, 2 ga watan Disamba aka buga wasan kwallo na bikin.

Har ila yau an yi taron kamun amarya a jiya Laraba, inda masoyan suka fito shar dasu cikin shiga ta kamala da kasaita.

Hotunan kamun auren jarumin Kannywood, Nuhu Abdullahi
Hotunan kamun auren jarumin Kannywood, Nuhu Abdullahi Hoto: nuhuabdullahi
Asali: Instagram

An gano amaryar sanye da kayan al’ada ta Fulani mai launin bula inda shi kuma angon ya sanya dakakkiyar shadda dinkin babban riga shima launin bula.

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun kashe mutum daya, sun yi garkuwa da wasu 5 a jihar Niger

Legit.ng ta gano kasaitattun hotunan bikin wanda jarumin ya wallafa a shafinsa na Instagram.

A ranar yau Juma’a, 4 ga watan Disamba ne dai za a kulla aure a shari’ance tsakanin jarumin da tauraruwar zuciyarsa.

Za a daura auren ne bayan sallar Juma’a a babban masallacin Alfurqan da ke Alu Avenue, Nasarawa G.R.A Kano.

Ga karin hotuna na bikin a kasa:

KU KARANTA KUMA: EndSARS: Gwamnan Legas ya baiwa kowanne cikin iyalan yan sandan da aka kashe N10m

A gefe guda, an gano bidiyon wata amarya da angonta kwanan nan a shafin soshiyal midiya kuma ya samu martani na ban dariya daga yan Najeriya.

Bidiyon ya nuno wasu ma’aurata a wajen liyafar aurensu. Da aka kai lokacin ciyar da ango sai aka gano sabuwar amaryar ta tsuguna kan gwiwowinta yayinda shi kuma angon ya zauna kan wani kayataccen kujera fari.

Kyakyawar amaryar, wacce ke sanye da kaya launin ja, ta dibi abinci a hannunta don ciyar da angonta.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng