Yan bindiga sun kashe mutum daya, sun yi garkuwa da wasu 5 a jihar Niger

Yan bindiga sun kashe mutum daya, sun yi garkuwa da wasu 5 a jihar Niger

- Masu garkuwa da mutane sun kai farmaki garin Bwari-Sabo da ke karamar hukumar Tafa na jihar Niger

- Yan bindigan sun halaka wani bawan Allah tare da yin garkuwa da wasu biyar

- Shugaban karamar hukumar, Ibrahim Mami Ijah, ya tabbatar da afkuwar lamarin inda yace yana cikin alhini

Wasu da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun harbi mutum daya sannan sun yi garkuwa da wasu mutum biyar a garin Bwari-Sabo da ke karamar hukumar Tafa na jihar Niger.

Wani mazaunin yankin, wanda ya bayyana sunansa a matsayin Shuaibu, ya ce lamarin ya afku ne da misalin karfe 12:00am lokacin da yan bindigan su da yawa suka farma garin.

Ya ce yan bindigan sun bude wuta a bangarori daban-daban bayan sun kakkabe wasu gidaje a yankin, cewa sun harbi wani mazaunin yankin da yayi yunkurin tserewa ta kofar bayan gidansa inda ya mutu a nan take

Yan bindiga sun kashe mutum daya, sun yi garkuwa da mutum 5 a jihar Niger
Yan bindiga sun kashe mutum daya, sun yi garkuwa da mutum 5 a jihar Niger Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

A cewar Shuaibu, masu garkuwa da mutanen sun kai farmaki gidaje uku, sun kashe mutum daya sannan suka waske da mutum biyar cikin daji.

KU KARANTA KUMA: Dan APC daya tilo da za ku iya aminta dashi matacce ne, Melaye ya gargadi yan PDP

“Daya mutumin da ya mutu ya yi kokarin tserewa ne ta kofar baya, bai san cewa daya daga cikin yan bindigan ya boye a baya ba inda shi kuma ya bude masa wuta,” in ji shi.

Ya ce an kai marigayin asibitin dake yankin daga bisani inda aka tabbatar da mutuwarsa.

Shugaban karamar hukumar ta Tafa, Ibrahim Mami Ijah, ya tabbatar da lamarin ta wayar tarho, sai dai bai yi wani dogon jawabi ba, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

“Yan bindigan sun kai mamaya Bwari-Sabo da misalin karfe 2:00 na safe amma ba zan iya dogon jawabi kan lamarin ba a yanzu domin har yanzu ina cikin jimami,” in ji shi.

An tattaro cewa Bwari-Sabo na amfani da iyaka daya da yankin Bwari na birnin tarayya.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Sabon jirgin yakin da Nigeria ta saya ya iso kasar

A gefe guda, rundunar yan sanda ta tabbatar da mutuwar mutum daya tare da garkuwa da wasu mutum takwas a garin Gwaram, karamar hukumar Talatan Mafara a jihar Zamfara.

Mayakan sun far ma kauyen a kan babura su da yawa da misalin karfe 3:00 na tsakar daren ranar Litinin sannan suka dunga bi gida-gida suna sace mazauna garin, Channels TV ta ruwaito.

Da yake tabbatar da lamarin, kakakin yan sandan jihar Zamfara, Shehu Mohammed ya ce wadanda aka sace harda matar hakimin garin.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng