Ango ya fusata bayan amarya ta cinye abincin da aka tanada don shi a wajen liyafar aurensu (bidiyo)

Ango ya fusata bayan amarya ta cinye abincin da aka tanada don shi a wajen liyafar aurensu (bidiyo)

- An gano wani ango da ke cika yana batsewa a wajen liyafar bikinsa bayan abunda amaryarsa tayi

- Ya kamata amaryar ta ciyar da sabon angon nata abinci amma maimakon haka sai ta ambada a nata bakin

- An gano bakin da suka halarcin taron suna yi wa ma’auratan dariya

An gano bidiyon wata amarya da ango kwanan nan a shafin soshiyal midiya kuma ya samu martani na ban dariya daga yan Najeriya.

Bidiyon ya nuno wasu ma’aurata a wajen liyafar aurensu. Da aka kai lokacin ciyar da ango sai aka gano sabuwar amaryar ta tsuguna kan gwiwowinta yayinda shi kuma angon ya zauna kan wani kayataccen kujera fari.

Kyakyawar amaryar, wacce ke sanye da kaya launin ja, ta dibi abinci a hannunta don ciyar da angonta.

Ango ya fusata bayan amarya ta cinye abincin da aka tanada don shi a wajen liyafar aurensu (bidiyo)
Ango ya fusata bayan amarya ta cinye abincin da aka tanada don shi a wajen liyafar aurensu Hoto: @ijeomadaisy
Source: Instagram

Sai dai kuma, da lokacin zubawa mijin abinci a bakinsa yayi inda ya riga ya bude shi, sai amaryar tayi saurin janye hannunta sannan maimakon haka sai ta zuba a nata bakin.

KU KARANTA KUMA: Dattawan arewa na nan akan bakarsu na neman Buhari ya sauka, In ji Hakeem Baba Ahmed

Abunda amaryar tayi ya fusata angon nata sannan wata bakuwa a bayan angon ta kara tunzura lamarin ta hanyar yi masa dariya.

Kalli bidiyon ban dariyar a kasa:

Martanin yan Najeriya game da bidiyon:

kambeaut.y:

“Ya yi kaman zai mangareta, amma ya kasa saboda taron jama’a.”

naijaplayboi:

“Na rantse wannan gayen zai dunga dukan mata. Kalli jijiyoyin kansa yadda suka fito cikin kasa da sakan biyu.”

imagobelle:

“Irin wannan miji da bai san wasa ba ehn.”

amyk_8890:

“Kalli fusataccen fuskarsa, kilan da ba a bainar jama’a bane da ya waska mata mari daya.”

A wani labarin, wasu masoya yan Najeriya sun sha gagarumin suka bayan bayyanar hoton kafin aurensu wanda ya shahara a shafin Twitter.

A hoton wanda ya haddasa cece-kuce a yanar gizo, an gano ma’auratan tsaye a kan hanyar jirgin kasa, yayinda matashin ya daura zani a kugunsa, ita kuma amaryar ta nada nata a wuya kamar riga.

KU KARANTA KUMA: Dan APC daya tilo da za ku iya aminta dashi matacce ne, Melaye ya gargadi yan PDP

Matashin, wanda ya tsaya dan tazara kadan tsakaninsa amaryar tasa, yana sanye da na’urar aika iska ta oksijin zuwa ga matashiyar.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel