Yan bindiga sun kashe hakimi, sun yi garkuwa da wasu mutum 8 a Zamfara

Yan bindiga sun kashe hakimi, sun yi garkuwa da wasu mutum 8 a Zamfara

- Wasu yan bindiga sun kai farmaki garin Gwaram da ke karamar hukumar Talatan Mafara a Zamfara

- Sun halaka hakimin kauyen sannan suka yi garkuwa da wasu mutane takwas

- Kakakin rundunar yan sandan jihar, ya tabbatar da afkuwar lamarin

Rundunar yan sanda ta tabbatar da mutuwar mutum daya tare da garkuwa da wasu mutum takwas a garin Gwaram, karamar hukumar Talatan Mafara da ke jihar Zamfara.

Mayakan sun far ma kauyen a kan babura su da yawa da misalin karfe 3:00 na tsakar daren ranar Litinin sannan suka dunga bi gida-gida suna sace mazauna garin, Channels TV ta ruwaito.

Da yake tabbatar da lamarin, kakakin yan sandan jihar Zamfara, Shehu Mohammed ya ce wadanda aka sace harda matar hakimin garin.

Yan bindiga sun kashe hakimi, sun yi garkuwa da wasu mutum 8 a Zamfara
Yan bindiga sun kashe hakimi, sun yi garkuwa da wasu mutum 8 a Zamfara Hoto: @PremiumTimesng
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Sabon jirgin yakin da Nigeria ta saya ya iso kasar

Har ila yau ya ce akwai tsohon shugaban PDP na gudunmar, Musa Makeri cikin wadanda aka yi garkuwa da su.

Ya ce yan bindigan sun harbe hakimin garin har lahira bayan ya yi bari su yi garkuwa da shi , da kuma fadin cewa ya gwammaci a kashe shi a garinsa a kan a kai shi jeji.

A gefe daya kuma, kungiyar dattawan arewa ta sake sabonta kiran da take yi na neman Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi murabus.

Da yake magana a yayin hira da Channels Television a ranar Laraba, 2 ga watan Disamba, kakakin kungiyar, Hakeem Baba-Ahmed, ya ce hujjojin da ke kasa sun marawa kiraye-kiraye da suke yi ga Shugaban kasar yayi murabus a baya.

KU KARANTA KUMA: Dan APC daya tilo da za ku iya aminta dashi matacce ne, Melaye ya gargadi yan PDP

Ya ce: “Hujjar da ke kasa ya marawa abunda muke fadi baya. Shugaban kasar ya yi rantsuwa da Al-Qur’ani don kare al’umman kasar. Ya gaza yin hakan.

“Wannan shine shekararsa ta biyar a kan mulki. Halin da ake ciki yana kara tabarbarewa a karkashinsa kuma babu alama da ke nuna abubuwa za su inganta.”

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng