Dan APC daya tilo da za ku iya aminta dashi matacce ne, Melaye ya gargadi yan PDP
- Sanata Melaye ya shawarci takwarorinsa a PDP a kan sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki
- Tsohon dan majalisar ya bayyana cewa babu wani dan APC da ke raye da ya cancanci a aminta da shi
- Shawarar Melaye ya biyo bayan hasashen da ke kara yawa na yiwuwar sauya shekar yan PDP zuwa APC
Dino Melaye, tsohon sanatan da ya wakilci yankin Kogi ta yamma a majalisar dattawan kasar, ya ba yan jam’iyyar Democratic Party (PDP) da ke shirin sauya sheka zuwa All Progressives Congress (APC) mai mulki.
Melaye ya bayar da shawarar ne a cikin wani wallafa da yayi a shafin Twitter wanda Legit.ng ta gano a ranar Laraba, 2 ga watan Disamba.
Jigon na PDP wanda shima ya dawo jam’iyyar adawar ne daga APC a 2018 ya gargadi takwarorinsa a kan shirin sauya sheka.
Ya wallafa a Twitter:
“Wadanda ke shirin barin PDP, shawarata gareku ta gaskiya. Dan APC daya tilo da za ku iya aminta da shi shine mataccen dan APC. Kada ku bari a shashantar da ku."
KU KARANTA KUMA: Dan Allah ka fito takarar Shugaban kasa a 2023, majalisar dokokin Kogi ta roki Gwamna Bello
KU KARANTA KUMA: Dattawan arewa na nan akan bakarsu na neman Buhari ya sauka, In ji Hakeem Baba Ahmed
Furucin Melaye ya biyo bayan sauya shekar da Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi yayi kwanan nan daga PDP zuwa APC.
Biyo bayan koken da ya sanya shi sauya sheka, Gwamna Umahi ya ce ya koma APC ne saboda zargin PDP da rashin yiwa yankin kudu maso gabas adalci.
A cewar gwamnan, bai yi danasani ba game da komawarsa APC.
A gefe guda, sauyin-shekar da gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi ya yi, ya yunkuro da gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle a kan barin jam’iyyar PDP.
Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa Bello Matawalle ya fito ya yi magana bayan Dave Umahi ya tsere daga PDP, ya koma jam’iyyar APC mai mulki.
Da ya ke jawabi ta bakin wani hadiminsa da ke taimaka wa wajen hulda da jama’a, Zailani Bappa, gwamnan adawan ya yabi matakin da Umahi ya dauka.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng