Yanzu Yanzu: Sabon jirgin yakin da Nigeria ta saya ya iso kasar

Yanzu Yanzu: Sabon jirgin yakin da Nigeria ta saya ya iso kasar

- Rundunar NAF na ci gaba da jajircewa a kokarin da take wajen yaki da ta’addanci da sauran miyagun ayyuka

- A cikin haka, rundunar sojin saman ta karbi jirginta mai saukar ungulu kirar Mi-171E daga Serbia a ranar Laraba, 2 ga watan Disamba

- Wannan ne jirgin yaki na biyu kirar Mi-171E da gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta saya

Rundunar sojin sama (NAF) a kokarinta na yin maganin Boko Haram, yan fashi da makami da sauran miyagun ayyuka a kasar ta karbi wani babban madogara.

A ranar Laraba, 2 ga watan Disamba, NAF ta karbi sakon jirginta na biyu mai saukar ungulu kirar Mi-171E wanda gwamnatin tarayya ta siya daga kasar Serbia.

Rundunar NAF ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da Legit.ng ta samu daga kakakinta, Air Commodore Ibikunle Daramola.

Yanzu Yanzu: Sabon jirgin yakin da Nigeria ta saya ya iso kasar
Yanzu Yanzu: Sabon jirgin yakin da Nigeria ta saya ya iso kasar Hoto: @NigAirForce
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Ango ya fusata bayan amarya ta cinye abincin da aka tanada don shi a wajen liyafar aurensu (bidiyo)

Jirgin dabarun yaki na Ilyushin 76 ne ya kawo sabon jirgin mai saukar ungulu da misalin karfe 3:15 na rana a sansanin rundunar da ke Makurdi.

Air Vice-Marshal Olusegun Philip, ne ya tarbi jirgin a madadin Shugaban hafsan sojin sama, Air Marshal Sadique Abubakar.

Sabon jirgin yakin shine jirgin yaki na biyu kirar Mi-171E da gwamnati mai ci ta siya. Gaba daya kenan an siyi sabbin jiragen yaki 23 tun daga 2015.

Wata tawaga daga sashin siyan kayayyaki da taimakon masu gyara na NAF za su ajiye sabon jirgin yakin a Makurdi, kafin a gwada tashinsa da kuma shigar da shi rundunar NAF a hukumance.

KU KARANTA KUMA: Dattawan arewa na nan akan bakarsu na neman Buhari ya sauka, In ji Hakeem Baba Ahmed

A wani labarin, rundunar sojojin Najeriya ta dauki mataki kan yan ta’adda a Borno yan kwanaki bayan sun yi wa bayin Allah kisan kiyashi a jihar.

A cewar hedkwatar tsaro a ranar Talata, 1 ga watan Disamba, dakarun sojin Operation Lafiya Dole sun lalata mafakar shugabannin Boko Haram a dajin Sambisa.

A yayin aikinsu, rundunar sojin saman sun kuma kashe mayakan kungiyar da dama a Yale da ke jihar.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel