Bello Matawalle yana neman sauya-sheka daga PDP, ya yi takarar 2023 a APC

Bello Matawalle yana neman sauya-sheka daga PDP, ya yi takarar 2023 a APC

- Da alama APC ta karkata kan Gwamnan Zamfara bayan Umahi ya tsere daga PDP

- Ana zargin manyan APC suna neman Bello Matawalle ya koma jam’iyya mai mulki

- Rade-radi sun ce Gwamnan ya shirya barin PDP, Jagororin jam’iyya suka lallabe shi

Sauyin-shekar da gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi ya yi, ya yunkuro da gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle a kan barin jam’iyyar PDP.

Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa Bello Matawalle ya fito ya yi magana bayan Dave Umahi ya tsere daga PDP, ya koma jam’iyyar APC mai mulki.

Gwamna Bello Matawalle ya jinjina wa sauyin-shekar da takwaransa ya yi zuwa jam’iyyar APC.

KU KARANTA: Jam’iyyar PDP ta tsiyace, shiyasa ake barinta ana sauya-sheka

Da ya ke jawabi ta bakin wani hadiminsa da ke taimaka wa wajen hulda da jama’a, Zailani Bappa, gwamnan adawan ya yabi matakin da Umahi ya dauka.

Gwamnan na Zamfara ya bayyana cewa idan aka cigaba da irin wannan tafiya a PDP, zuwa zaben 2023, jam’iyyar hamayyar ba za ta iya kai wani labari ba.

Gwamnan da ya samu mulki a sakamakon hukuncin kotu, yana da alaka mai kyau da manyan APC a Zamfara irinsu Ahmed Sani Yarima da Kabiru Marafa.

A wata hira da aka yi da tsohon Sanatan Zamfara, Ahmed Sani Yarima, ya bayyana cewa gwamna Matawalle ya na daf da barin PDP, ya shigo tafiyar APC.

KU KARANTA: ‘Dan Jam’iyya ya tika Shugabannin PDP a kotu a rikicin Ebonyi

Bello Matawalle yana neman sauya-sheka daga PDP, ya yi takarar 2023 a APC
Bello Matawalle Hoto: www.premiumtimesng.com
Source: UGC

Rahotanni sun ce tsoron rasa kujerarsa ya hana gwamnan barin PDP tun tuni, domin kotu ta ba jam’iyyar da ta zo na biyu nasara ne a zaben jihar Zamfara.

A wani kaulin kuma, Bello Matawalle ya ki shiga jam’iyyar APC ne a dalilin rigimar da jam’iyyar ta ke fama da ita tsakanin Abdulaziz Yari da Kabir Marafa.

Jaridar ta ce a baya gwamnan ya rudu da barin PDP, daga cikin abin da ya sa Matawalle ya lafa da maganar canza-sheka shi ne yawan masu harin tikitin APC.

A makon jiya kun ji cewa jigon PDP a kudancin Najeriya, Bode George, ya soki zaman da su Cif Bisi Akande su kayi da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Babban ‘Dan adawar ya ce tattaunawar da aka yi a Aso Villa ba ta wuce maganar Bola Tinubu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel