Fatara, rashin biyan albashi da rigimar shugabanci suke addabar PDP inji APC

Fatara, rashin biyan albashi da rigimar shugabanci suke addabar PDP inji APC

- APC ta ce PDP ta gaza rike gurbin babbar Jam’iyyar hamayya a Najeriya

- Mai magana da bakin APC ya ce PDP ta tsiyace, shiyasa ake kaurace mata

- Yekini Nabena ya ce bai kamata a rika siyasa babu lafiyayyar hamayya ba

Jam’iyyar APC mai mulki ta ce PDP mai hamayya a Najeriya tana rasa dinbin mabiya ne saboda fatara ta kama ta, ba ta iya daukar nauyin kanta.

APC ta kuma bayyana cewa ‘yan adawa suna barin jam’iyyar PDP suna koma wa APC ne a dalilin rikicin shugabanci da yake damunta a halin yanzu.

Kamar yadda jaridar Punch ta bayyana, APC ta bayyana wannan ne a wani rubutu da mataimakin sakataren yada labaranta, Mista Yekini Nabena ya yi.

KU KARANTA: An nemi Majalisa ta tsige Gwamna kan barin PDP

Yekini Nabena daga garin Abuja, ya yi wa rubutun nasa da take “Abin da yasa masu son cigba a PDP suke tattara wa su na shigo wa jam’iyyar APC.”

Ya ce: “Ba abin mamaki bane wasu masu ra’ayin kawo cigaba daga cikin ‘ya ‘yan PDP suna dandazo, suna sauya-sheka zuwa APC a kwanakin nan.”

“A ce jam’iyyar da ba ta iya dawainiyar sakatariyarta, da biyan albashin ma’aikata, sannan shugabanninta su na fuskantar barazana, rashin adalci ne ayi tunanin masu son cigaba a cikin ‘ya ‘yanta za su cigaba da zama a PDP da ta gaza zama babbar jam’iyyar hamayya a Najeriya.”

Nabena ya ce jam’iyyar APC ba ta jin dadin abin da yake faruwa a siyasar kasar. “Abin takaici ne ganin PDP ta na neman maida Najeriya ta zama kasa mai aiki da jam’iyya guda..."

Fatara, rashin biyan albashi da rigimar shugabanci suke addabar PDP inji APC
Yekini Nabena Hoto: www.pmnewsnigeria.com
Source: UGC

KU KARANTA: 2023: Dogara da Tinubu za su nemi tikitin APC

"...A matsayinmu na jam’iyya da ta yadda da tsarin damukaradiyya da siyasar cigaba, ba mu tare da wannan.”

Ya cigaba da cewa: “Don haka mu ke kalubalantar sauran jm’iyyun hamayya su maye gurbin PDP, domin mu na son ganin an taso mu a gaba, ana caccakar manufofinmu a cikin ilmi.”

Mun ji cewa bayan Dave Umahi ya sauya-sheka, APC ta na neman raba wasu jihohin adawa da PDP, Idan APC ta yi nasara, gwamnonin jam'iyyar hammayar za sa ragu.

A ‘yan kwankin kwanan nan APC ta karbi Gwamna David Nweze Umahi, Sanata Elisha Abbo da irinsu Barnabas Gemade; Rt. Hon. Yakubu Dogara, da su Dr. Alex Otti.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel