George: Maganar Tinubu aka yi a lokacin da manyan APC su ka hadu da Buhari
- Bode George ya soki zaman da su Bisi Akande su kayi da Shugaba Buhari
- Babban ‘Dan adawar ya ce tattaunawar ba ta wuce maganar Bola Tinubu
- George ya ja-kunnen shugaban kasa Buhari game da burin Tinubu a 2023
Tsohon mataimakin shugaban jama’iyyar PDP, Cif Bode George, ya yi magana game da ziyarar da wasu jiga-jigan APC su ka kai a fadar shugaban kasa.
Bode George ya yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari cewa ka da ya rudu da masu neman tallata masa tsohon gwamnan Legas, Bola Ahmed Tinubu.
Jagoran adawar, ya zargi manyan jam’iyyar APC da suka gana da shugaban kasar da laifin watsi da halin da Legas take ciki, sun buge da sha’anin siyasarsu.
KU KARANTA: Wasu suna so tsohon Gwamna Yari ya zama Shugaban APC
Cif George ya kuma yi kira na musamman ga Bisi Akande,cewa ya daina wahalar da kansa wajen yi wa wani mai neman mulkin kasar nan kamun-kafa.
‘Dan siyasar ya yabi tsohon gwamnan jihar Osun, Akande, wanda ya ce ya yi mulki da gaskiya.
A rubutun da ya yi, Bode George ya soki zaman da Bisi Akande, Prince Tajudeen Olusi, Dr Yomi Finnih, da Segun Osoba su kayi da shugaban kasa Buhari.
A cewar ‘dan adawar, akwai lauje cikin nadi a wannan ganawa da aka yi a fadar shugaban kasa.
KU KARANTA: Zan karbi mulki daga hannun Fintiri - Abbo
Bayan haka, Bode George ya zargi wani ‘dan siyasa da burin zama shugaban kasa ko ta wani irin hali, George bai boye cewa ya na yi ne da Bola Tinubu ba.
Ya ce tun da aka yi wannan taro babu Tinubu, to maganar da aka tattauna ba ta wuce a game da shi, sannan ya roki Akande ya rabu da maganar abokin na sa.
Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma ya fada wa Ibo sirrin karbar shugabancin Najeriya ba tare da an yi rikici ba, ya ce hanya mafi sauki ita ce ta lalama.
Uzodimma ya na ganin dumin kirji da zafin kai ba zai kai ‘Yan siyasar Ibo ga kujerar mulki ba.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng